Mummunar Gobara Ta Lakume Wureren Shakatawa 4 a Jihar Kano
- Rahotanni sun kawo cewa mummunar gobara ta tashi a wuraren shakatawa hudu a jihar Kano
- Gobarar wacce ta afku sakamakon tartsatsin wutar lantarki ta yi barna sosai a wuraren
- Da yake tabbatar da lamarin, mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abudullahi, ya ce sun tura jami'ansu don shawo kan lamarin
Jihar Kano - Labari da ke fitowa daga jihar Kano shine cewa mummunar gobara ta tashi a wuraren shakatawa hudu na Audu Bako gefen asibitin koyarwa na Muhammad Abudullahi Wase (MAWTH).
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, gobarar ta lalata wajen shakatawar gaba daya.
Gobarar ta yi barna sosai, hukumar kashe gobara ta jihar Kano
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abudullahi, wanda ya bayyana hakan, ya ce an tura jami'an hukumar da dama zuwa wurin da abun ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Abdullahi ya kuma bayyana cewa gobarar ta yi mummunar barna a wuraren shakatawar.
Ya ce:
"Mun fito da jami'anmu daga tashoshin kashe gobara daban-daban, ciki har da babban ofishin kashe gobara, zuwa wurin da lamarin ya faru, domin shawo kan gobarar da ta yi illa sosai ga wuraren shakatawar.”
Ya kara da cewar gobarar ta tashi ne sakamakon tartsatsin wutar lantarki daga kicin mallakin gidan abincin KGC ne.
Gobara ta kone shaguna 80 a Kano
A wani labari makamancin wannan, mun kawo a baya cewa wata gobara da ta tashi ranar Laraba 1 ga watan Maris a kasuwar Kurmi da ke Kano, ta lalata shaguna 80.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin 5:23 na asuba daga wani Aliyu Alkasim game da tashin gobarar.
Gobara ta tashi a kasuwar Samsung
Haka kuma, mun ji cewa wata mummunar gobara ta tashi a daya daga cikin manyan shagunan da ke sayar da kayan kamfanin Samsung a Abuja.
Gobar ta tashi ne a daren ranar Litinin, kamar yadda rahoton jaridar Leadership ya bayyana.
Babban shagon wanda ya ke a yankin Banex da ke gundumar Wuse 2, cikin kwaryar babban birnin tarayyar Najeriya, ya kama da wuta gadan-gadan ba tare da an iya shawo kanta ba.
Asali: Legit.ng