Na Yi Mamakin Abinda Tsaffin Ministocin Buhari Ke Fada Game Da Shi, Rabaran Kukah

Na Yi Mamakin Abinda Tsaffin Ministocin Buhari Ke Fada Game Da Shi, Rabaran Kukah

  • Bishop Mathew Kukah ya bayyana babban matsalarsa da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Malamin addinin ya bayyana cewa ba shi da wata matsala ta kashin kai da Buhari, illa dai bai ji dadin salon shugabancinsa ba
  • Bishop Kukah ya kuma bayyana cewa ya kadu da jin yadda ministocin Buhari suke magana game da tsohon shugaban kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Sokoto - Limamin cocin Katolika na Sokoto, Rabaran Mathew Kukah, ya bayyana wani abin mamaki game da tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Bishop Kukah ya ce bai da matsala da Buhari
Na Yi Mamakin Abinda Tsoffin Ministoci Ke Fallasa Wa Game da Buhari, Malamin Arewa Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Bishop Kukah ya magantu kan gwamnatin Buhari

A wata hira da aka yi da shi, malamin ya bayyana cewa ya kadu da jin abun da ministocin tsohon shugaba Buhari suke fadi game da shi da gwamnatinsa.

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira a gidan talbijin na Arise a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Fubara ya gana da Wike, Ya ce ‘mai gida na har gobe’

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kukah wanda ya kasance daya daga cikin masu sukar Buhari da gwamnatinsa, ya bayyana cewa bai da wata matsala ta kashin kai da tsohon shugaban kasar, rahoton Vanguard.

“Ba wani abu da na fadi game da Shugaba Buhari na kashin kai, wanda ke nuna rashin mutuntawa, kawai dai na ji cewa yana yin wasu abubuwa, musamman a fannin tafiyar da al'amuran mu.
"Ina magana da ministoci da suka yi a wannan gwamnati yanzu, ba zan iya kiran sunaye ba. Na kadu da jin irin abubuwan da mutane ke fadi game da wadanda suka yi aiki a wancan gwamnati; za a yi magana kan wannan wata rana," inji shi.

Kukah ya bayyana babban matsalarsa da Buhari

Da yake ci gaba da magana, Bishop Kukah ya ce matsalarsa da Buhari shine rashin iya tafiyar da al’amuran kasar.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun musulunci ta umurci magidanci ya karbi ɗan da ya ke kokwanton ba nasa bane

Malamin ya yi ikirarin cewa tsohon shugaban kasar ya kara jefa Najeriya cikin mawuyacin hali kuma ya yi nasarar raba kasar.

Femi Adesina ya caccaki Kukah

A wani labarin, mun ji cewa hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya caccaki Matthew Hassan Kukah kan kushe gwamnatin Muhammadu Buhari.

Kukah ya kushe salon gwamnatin tsohon shugaba Buhari ne yayin bikin cikan shekaru 60 na Afe Babalola a matsayin lauya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng