Kamar Wasa, Wata Mata Ta Koma Yin Rarrafe a Taron Biki, Bidiyon Ya Girgiza Intanet
- Bidiyon wata mata tana rarrafe a wajen wani taro ya bayyana a soshiyal kuma ya jefa mutane cikin rudani
- Lafiyar na tafiyarta lafiya kalau a tsaknin wasu mata biyu kwatsam sai aka ga ta koma yin faffare a kasa
- Mutane da dama sun yi mamakin muhimmanci ko dalilinta na yin haka, inda wasu suka yi martani a kan tufafin jikinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jama'a sun yi cece-kuce kan bidiyon wata mata da ke rarrafe a kasa a wajen wani taron biki.
Shafin @cubeyd90 ne ya wallafa bidiyon a TikTok kuma ya jefa masu amfani da intanet cikin rudani yayin da mutane ke neman amsoshi kan abun da ya faru.
A cikin bidiyon wanda ya samu mutum miliyan hudu da suka kalle shi, matar ta fara tafiyarta lafiya kalau a tsakanin wasu mata biyu lokacin da ta yi kasa.
Cikin yan sakwanni, sai ta fara rarrafe a kasa. Ta rarrafa har sai da ta kai wajen kafar wata da ta fita yawan shekaru wacce ke zaune kan kujera a gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta sumbaci kafar matar sannan sai ta rungume ta. Yayin da suka rungume juna, wata mata ta fito sannan ta fara lika masu kudi.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun shiga rudani
S€T£M! ta ce:
"Ba nice amaryar ba nice mai kallon amaryar da tsaki a TikTok."
Fozi ta ce:
"Mahaifiyata na matukar sona da ba za ta bari na yi wannan ba."
Sabira ta ce:
"Yi hakuri ban taba ganin abu mai kama da wannan a al'adarmu ba."
Cee-wai 001 ta ce:
"Matar da ke watsa kudi....menene wannan."
joonhoe ta ce:
"Ina tunanin dole sai ta yi rarrafe sannan ta duka don samun amincewar uwargidar."
Blinks@official ta ce:
"Idan kan ku ya kulle kamar nawa mu hadu a nan."
Daraunusual ta ce:
"Tana rokon uwar mijin kada ta wargaza mata aurenta cewa soyayya daya ce."
Miji ya je bikon mata da tsire
A wani labari na daban, mun ji cewa wani bidiyo mai ban dariya na sabanin ma'aurata da sulhunsu ya yadu a dandalin soshiyal midiya.
Ya nuna yadda miji ya yi baikon matarsa wacce ta yi yaji bayan sun samu zazzafan sabani a tsakaninsu da tsire.
Asali: Legit.ng