An Dakatar da Jiragen Sama Fita Ko Zuwa Imo, an Haramta Wa Gwamna Uzodinma Yin Tafiya a Jirgi
- Rahotanni sun bayyana cewa kungiyoyin sufurin jiragen sama sun janye aiki akan duk wani jirgi da zai tashi daga Imo ko zai sauka jiha
- Wannan matakin ya biyo bayan umurnin da kungiyoyin NLC da TUC suka fitar na shiga yajin aiki a fadin Najeriya, sakamakon farmakar shugaban kungiyar NLC a Imo
- Kungiyoyin masana’antar jiragen saman da suka hada da NUATE, ATSSSAN, ANAP da kuma NAAPE suka bayar da umurni, inda zai fara aiki a daren ranar Laraba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kungiyoyin kwadago a masana’antar sufurin jiragen sama sun bayar da umarnin janye ayyukansu a kan duk wani jirgi da zai tashi zuwa garin Owerri, jihar Imo, a kafatanin filayen jiragen saman Najeriya.
Wannan dai na zuwa ne a matsayin 'bin umarnin' kungiyar kwadago da ta kunshi kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC bayan cin zarafin shugaban NLC, Joe Ajaero a makon da ya gabata a Owerri.
Kungiyoyin masana’antar jiragen saman da suka hada da kungiyar ma’aikatan sufurin jiragen sama ta kasa (NUATE), kungiyar manyan ma’aikatan sufurin jiragen sama (ATSSSAN), kungiyar shahararru a fannin sufurin jiragen sama ta kasa (ANAP) da kuma kungiyar matuka da injiniyoyin jirage ta (NAAPE), sun bayyana haka. a cikin sanarwar hadin gwiwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar hadin guiwar, dauke da sa hannun manyan sakatarorin kungiyoyin da suka hada da Comrades Ocheme Aba; NUATE, Frances Akinjole; ATSSSAN, Abdul Rasaq Saidu; ANAP da Umoh Ofonime, NAAPE, ta kuma bayyana Gwamna Hope Uzodimma a matsayin wanda ba a maraba da shi a dukkan filayen jiragen sama na kasar.
Sanarwar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ta ci gaba da cewa:
“Bayan ta’addancin da gwamnatin jihar Imo ta Hope Uzodimma ta yi wa ma’aikata da kuma ci gaba da nuna halin ko in kula kan lamarin; tare da kuma bin umarnin matsayar da aka cimma wa a taron hadin gwiwa kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC), kungiyoyin ma'aikatan sufurin jiragen sama da aka ambata a sama, wadanda ke karkashin NLC da TUC, sun umurci dukkan ma’aikatan jiragen sama (na gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu), da su janye duk wani aiki da su ke yi akan jiragen Owerri (na shiga ko na fita) daga kowane filin jirgin sama a Najeriya, daga daren ranar 8 ga watan Nuwamba (yau).
“Bugu da kari, mun ayyana Hope Uzodimma, Gwamnan Jihar Imo a matsayin wanda ba ma maraba da shi a duk tashoshin jiragen sama na Najeriya har sai ya yi nadama akan danyen aikin da ya aikata.
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
“Kungiyoyin mu za su kara daukar wani matakin ta hanyar hadin gwiwa da kasashen duniya don hana Hope Uzodimma yin tafiye tafiye a jiragen sama.
“Da wannan ne kuma mu ke ba dukkanin ma'aikatan sufurin jiragen sama na filin jirgin Sam Mbakwe International da ke Owerri, da su shiga yajin aiki, kowa ya zauna a gida, daga daren yau Litinin, 8 ga watan Nuwamba, 2023, domin bin umurnin kungiyoyin NLC and TUC.
NLC da TUC za su tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya
Shuwagabannin kungiyoyin kwadago na Nigeria Labour Congress (NLC) da kuma Trade Union Congress (TUC) sun ayyana kudirin shiga yajin aikin sai baba ta gani a fadin Najeriya. Kungiyoyin za su shiga yajin aikin a ranar Talata mai zuwa, 14 ga watan Nuwamba, 2023.
Shuwagabannin kungiyoyin biyu sun cimma wannan matsayar ne a wani babban taro na shuwagabannin kungiyoyin da suka gudanar ranar Talata a Abuja, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng