Shugaba Tinubu Ya Yi Sabbi Nade-Nade Guda 3, Jerin Sunayensu Ya Bayyana

Shugaba Tinubu Ya Yi Sabbi Nade-Nade Guda 3, Jerin Sunayensu Ya Bayyana

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin sabbin kwamishinonin zartaswa guda uku da za su yi aiki a hukumar kula da man fetur ta Najeriya (NUPRC)
  • Hukumar ta NURPC tana sa ido kan masana'antar man fetur da iskar gas don tabbatar da bin ƙa'idoji da dokokin da suka dace
  • Har ila yau, tana kula da tsaro da sauran ƙa'idojin da suka shafi fitarwa da shigo da kayayyakin man fetur cikin ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu a ranar Talata, 7 ga watan Nuwamba, ya amince da naɗin sabbin kwamishinonin zartaswa guda uku da za su yi aiki a hukumar kula da man fetur ta Najeriya (NUPRC).

Kara karanta wannan

Hukuncin kotun koli: An ba Peter Obi shawarar abin da ya kamata ya yi wa Shugaba Tinubu

Shugaba Tinubu ya kuma bayyana sauya wa wani kwamishina wurin aiki har sai majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da naɗinsu.

Shugaba Tinubu ya yi sabbin nade-nade
Shugaba Tinubu ya yi sabbin nade-nade a hukumar NUPRC Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Tinubu ya naɗa sabbin kwamishinonin NUPRC guda 3

Tun bayan rantsar da shi a watan Mayu, Shugaba Tinubu mai shekaru 71 ya yi naɗe-naɗen mukamai. Waɗannan naɗe-naɗen dai yana yin su ne domin tabbatar da cewa shugaban kasar ya aiwatar da ajandar sa ta ‘Sabunta fata' da ya yi wa ƴan Najeriya alƙawari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga jerin sunayensu:

1. Bashir Indabawa - Arewa maso Yamma, kwamishinan haƙowa da kula da filaye.

2. Dr. Kelechi Ofoegbu - Kudu maso Gabas, Babban kwamishinan ayyuka da gudanarwa (wanda aka sauya wa wajen aiki).

3. Enorense Amadasu - Kudu maso Kudu, Babban kwamishinan cigaba.

4. Babajide Fasina — Kudu maso Yamma, Babban kwamishinan ƙa’idojin tattalin arziƙi da dabarun tsare-tsare.

Kara karanta wannan

Matsala ta tunkaro, ƙungiyoyin ƙwadago NLC da TUC sun kira babban taron NEC kan wasu batutuwa

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale, ya fitar, ta ce shugaba Tinubu ya amince da yin garambawul a hukumar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Shugaban ƙasa ya amince da wannan garambawul bisa la'akari da zurfin saninsa game da duk abubuwan da suka shafi fannin da nufin kafa tsarin kawar da mummunar dabi'a tare da karfafa himma da ayyukan kasuwanci na bisa tsarin doka a cikin masana'antar."

Tinubu Ya Yi Nadi a Fannin Lafiya

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wani muhimmin naɗi a fannin harkar lafiya.

Tinubu ya naɗa Dakta Abdu Mukhtar a matsayin kodinetan cibiyar lafiya ta ma'aikatar lafiya ta Tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng