Hukumar Hisbah a Kano Ta Kori Wannan Babban Kwamandanta, Ta Bayyana Dalili

Hukumar Hisbah a Kano Ta Kori Wannan Babban Kwamandanta, Ta Bayyana Dalili

  • Hukumar Hisbah a jihar Kano ta ɗauki mataki kan ɗaya daga cikin kwamandojinta masu haɗa baki da masu otal
  • Shugaban hukumar Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana cewa an kori kuma kwamandan kuma ana nemansa ruwa ajallo
  • Daurawa ya yi nuni da cewa kwamandan yana haɗa baki ne da masu otal domin kada jami'an hukumar su kai musu sumame

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kori ɗaya daga cikin kwamandojin ta saboda haɗa baki da yin zagon ƙasa a yaki da lalata da baɗala a jihar.

Babban kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa, ya tabbatar wa manema labarai hakan a ranar Talata a Kano, cewar rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Kano: Hisbah ta yi martani kan aske kan wata budurwa da kwalba, ta fadi matakin da ta dauka a kai

Hisbah ta kori kwamandanta a Kano
Hukumar Hisbah a Kano ta sallami kwamandanta Hoto: Hisbah Command
Asali: Facebook

Daurawa ya bayyana cewa ana kan gudanar da bincike kan wasu jami'an hukumar guda biyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi bayanin cewa ma’aikatan da aka kora galibi suna hada baki ne da "miyagun ɓata gari domin aikata munanan ayyukan baɗala a jihar."

Meyasa aka dakatar da kwamandan?

Daurawa ya ce da hawansa mulki, ya fara aiki gadan-gadan kan hanyar tsaftace hukumar daga baragurɓin jami'ai saboda yanzu hukumar ta kasance ba kamar da ba.

A kalamansa:

"Mun kori mataimakin sufeto na Hisbah (DSH) tare da bayyana cewa ana neman sa. Duk inda aka same shi a kama shi a gurfanar da shi a gaban kuliya."
"Ya kan haɗa kai da masu gudanar da otal domin kada hukumar Hisbah ta kai sumame a otal ɗin nasu a yayin gudanar da ayyukanta."
"Domin haka a lokacin da muka kai sumamen, masu otal ɗin da ake aikata irin wannan ta’asar, sun ji haushi cewa Hisbah ta canza."

Kara karanta wannan

Miyagu sun kai kazamin hari gidan babban jigon PDP kuma tsohon kwamishina, sun jefa bama-bamai

"Sun biya shi kudi domin kada ya yi aiki a otal ɗinsu. Akwai ɗaya daga cikin masu otal ɗin da ya tambaye mu me muke so su yi mana domin tallafa mana."
"Kuma mun gaya masa cewa gwamnati ta ɗora mana nauyin da ya rataya a wuyanmu, domin haka ita ce ke da alhakin gudanar da ayyukanmu."
"Don haka sai yake tambayar cewa me zai sa ya ba Hisbah kudi, kwatsam sai su juya masa baya su kai sumame a otal ɗinsa."

An Mayar da Daurawa Shugabancin Hisbah

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mayar da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa kan shugabancin hukumar Hisbah.

Gwamnan ya yi hakan ne bayan Sheikh Daurawa da wasu jami'an hukumar Hisbah sun yi murabus daga kujerarsu a watan Mayun shekarar 2019.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng