Ma'aikata Sun Sanar Da Sabon Ranar Fara Yajin Aiki Sai Baba Ta Gani Kan Lakadawa Shugaban NLC Duka

Ma'aikata Sun Sanar Da Sabon Ranar Fara Yajin Aiki Sai Baba Ta Gani Kan Lakadawa Shugaban NLC Duka

  • Shuwagabannin kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun sanar da kudirinsu na shiga yajin aikin sai baba ta gani a ranar Talata mai zuwa
  • Kungiyoyin sun yanke hukuncin shiga yajin aikin ne kwanaki kadan bayan da aka lakada wa shugaban kungiyar NLC dukan tsiya a jihar Imo
  • An yi wa Ajaero duka ne a lokacin da ya ke shirin jagorantar ma'aikatan jihar Imo gudanar da zanga-zangar nuna rashin goyon baya ga gwamnatin jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Shuwagabannin kungiyoyin kwadago na Nigeria Labour Congress (NLC) da kuma Trade Union Congress (TUC) sun ayyana kudirin shiga yajin aikin sai baba ta gani a fadin Najeriya. Kungiyoyin za su shiga yajin aikin a ranar Talata mai zuwa, 14 ga watan Nuwamba, 2023.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta tabbatar da Ministan Tinubu wanda ya lashe zaben sanata a jihar Arewa

Shuwagabannin kungiyoyin biyu sun cimma wannan matsayar ne a wani babban taro na shuwagabannin kungiyoyin da suka gudanar ranar Talata a Abuja.

Kungiyoyin kwadago da Shugaba Tinubu
Kungiyoyin sun yanke hukuncin tsunduma yajin aikin a wani taron gaggawa da suka gabatar a Abuja Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nigerian Labour Congress
Asali: Facebook

Kungiyoyin guda biyu sun ce tuni suka fara tattara kan mambobinsu domin ganin sun tsunduma yajin aikin ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan matakin na shiga yajin aiki ya biyo bayan dukan da aka lakada wa shugaban kungiyar NLC na kasa, Joe Ajaero, makon da ya gabata a jihar Imo.

Kungiyoyin NLC da TUC sun kira babban taron NEC

A ranar talata, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa kungiyoyin NLC da TUC sun kira taron gaggawa da nufin nazari kan yiwuwar tsunduma yajin aikin biyo bayan cin zarafin da aka yi wa shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, a jihar Imo.

Kara karanta wannan

Matsala ta tunkaro, ƙungiyoyin ƙwadago NLC da TUC sun kira babban taron NEC kan wasu batutuwa

A yain taron, sun tattauna da yin duba kan yarjejeniyar fahimta (MoU) da ƙungiyoyin kwadago suka rattaɓa wa hannu bayan cimma matsaya da gwamnati ranar 2 ga watan Oktoba.

A zaman taron ne, suka cimma matsayar fada wa yajin aikin a mako mai zuwa.

Shugaban NLC ya magantu kan yadda aka lakada masa duka

Kazalika, Legit ta ruwaito maku yadda shugaban kungiyar kwadago (NLC), Comrade Joe Ajaero, ya labarta yadda ya ci dukan tsiya a hannun jami'an tsaron da suka yi awon gaba da shi a ranar Laraba.

Ajaero ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafofin watsa labarai a ranar Alhamis, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.