Mummunar Gobara Ta Tashi a Babbar Kasuwar Sayar Da Kayan Samsung a Abuja

Mummunar Gobara Ta Tashi a Babbar Kasuwar Sayar Da Kayan Samsung a Abuja

  • Rahotanni sun bayyana cewa wata mummunar gobara ta tashi a wani babban shagon sayar da kayayyakin kamfanin Samsung a Abuja
  • Gobarar kamar yadda rahotanni suka bayyana ta tashi ne a daren ranar Litinin, a gundumar Wuse 2, kusa da katafaren shagon Banex
  • Gobarar ta tashi awanni kadan bayan da wata gobara ta tashi a ofishin jakadancin kasar Kanada da ke Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wata mummunar gobara ta tashi a daya daga cikin manyan shagunan da ke sayar da kayan kamfanin Samsung a Abuja.

Gobar ta tashi ne a daren ranar Litinin, kamar yadda rahoton jaridar Leadership ya bayyana.

Babban shagon wanda ya ke a yankin Banex da ke gundumar Wuse 2, cikin kwaryar babban birnin tarayyar Najeriya, ya kama da wuta gadan-gadan ba tare da an iya shawo kanta ba.

Kara karanta wannan

Likitoci sun yanke wa jarumin fina-finan Najeriya kafa don ceto ransa

Gobara shagon Samsung
Gobarar ta tashi ne a daren ranar Litinin, ba tare da sanin musabbabanin tashinta ba Hoto: @Abujacityng, @IamBlaccode
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ya zuwa wannan lokaci ba a san musabbabin tashin wutar ba.

Haka zalika mata majiya, ta bayyana cewa gobarar ta tsallaka zuwa wani gidan sayar da man fetur da ke makwaftaka da babban shagon.

Ofishin jakadancin Kanada ya kama da wuta a Abuja

A wani labarin makamancin wanna, wani bangaren ginin ofishin jakadancin kasar Kanada a Najeriya ya kama da wuta rigi-rigi a babban birnin tarayya Abuja ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa wasu sassan ofishin jakadancin Kanada wanda ke a lamba 13010G Palm Close, Diplomatic Drive, Central Business District a Abuja ne suka kama ci da wuta.

Sai dai har yanzun babu cikakken bayani kan ainihin abin da ya haddasa tashin wannan gobara a babban ofishin jakadancin na kasar waje.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa ban halarci zaman yanke shari’a a Kotun Koli ba, Peter Obi ya yi martani

Amma Hotunan da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda hayaki ke fitowa daga ginin.

Gobara ta lakume kadarorin miliyoyin naira a jihar Kwara

Kalika, anar ranar Asabar, 29 ga watan Yulin 2023, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda hukumar kashe gobara ta jihar Kwara ta kubutar da kadarorin da sun kai na N148.7m, lokacin da gobara ta kama rukunin wasu shaguna 20 a birnin Ilorin.

Gobarar wacce ta auku a dalilin tartsatsin wutar lantarki, ta laƙume kadara wacce ta fi ta N3.2m.

A cewar kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle, gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 05:57 na safiyar ranar kamar yadda rahoton Nigerian Trbune ya nuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.