Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Mahaifin Gwamna Soludo Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Mahaifin Gwamna Soludo Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Allah ya yi wa mahaifin Gwamna Soludo na jihar Anambra rasuwa da sanyin safiyar ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, 2023
  • Sakataren watsa labaran gwamnan, Christian Aburume, ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne bayan fama da jinya ta ɗan lokaci ƙanƙani
  • Ya ce mahaifin gwamnan ya rasu ya bar 'ya'ya maza bakwai da jikoki harda tattaɓa kunne, yana da shekaru 92 a duniya

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Anambra - Gwamnan jihar Anambra da ke Kudu maso gabashin Najeriya, Farfesa Chukwuma Soludo, ya rasa mahaifinsa, Pa Simeon Soludo (Ichie Akukananwa 1).

Gwamnan Anambra, Charles Soludo.
Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Mahaifin Gwamna Soludo Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Hoto: Charles Chukwuma Soludo
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta tattaro cewa mahaifin gwamna Soludo ya rasu ne da safiyar ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, 2023 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Makinde: Gwamnan PDP ya ciri tuta, ya yi ƙarin albashi mai tsoka ga ma'aikata da 'yan fansho

Sakataren watsa labaran gwamna Soludo na jihar Anambra, Christian Aburime, shi ne ya tabbatar da wannan rasuwa a wata sanarwa da ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, Pa Soludo (Mahaifin gwamna Soludo) ya rasu ya bar ‘ya’ya maza bakwai, surukai mata takwas, jikoki 22 da kuma tattaba-kunne shida.

Ya ce Gwamna Soludo ya bayyana cewa marigayi mahaifinsa ya yi rayuwa mai gamsarwa kuma ya rasu yana da shekaru 92 a duniya.

Mista Aburime, a cikin sanarwar da ya fitar, ya bayyana cewa za a sanar da jama'a karin bayani nan gaba kaɗan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Takaitaccen bayani kan Gwamna Soludo

Gwamna Soludo, wanda yana ɗaya daga cikin jagororin ƴan adawa a siyasar ƙasar nan, ya kasance gwamna ɗaya tilo na jam'iyyarAll Progressives Grand Alliance (APGA) .

Gabannin ya zama Gwamnan jihar Anambra, Soludo ya riiƙe matsayin gwamnan babban bankin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yayin da ake shirin yanke hukunci a Kano, IPAC ta tura sako ga Abba Kabir kan nade-naden mukamai

Idan baku manta ba a wasu shekaru mahara ɗauke da makamai sun yi garkuwa da mahaifin gwamnan a gidansa da ke Aguata.

A wani rahoton kuma Kanfanin wutar lantarki na Kaduna ya kori ma'aikatansa akalla 39 daga aiki bisa zargin aikata laifuka daban daban.

A wata sanarwa da kakakin kamfanin, Abdulazeez Abdullahi, ya fitar ya bayyana wasu daga cikin laifun da suka ja aka sallame su

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262