“Kasuwa Ta Yi Kyau”: Mabaraciya Ta Siya Soyayyar Kaza, Ta Darje Ta Zabi Wanda Take So

“Kasuwa Ta Yi Kyau”: Mabaraciya Ta Siya Soyayyar Kaza, Ta Darje Ta Zabi Wanda Take So

  • Wani bidiyon TikTok ya yadu, inda aka gano wata mata da ke bara a titi tana dudduba soyayyar kazar da wani ke talla
  • An gano matar wacce ke zaune a kasa kanta lullube da hijabi, tana zabo soyayyar kazar da aka yi wa yanka-yanka
  • Mai siyar da kazar ya tsaya tana kallo yayin da mabaraciyar ke zabo wanda take so daga bokitin tallan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wani bidiyon TikTok mai ban mamaki ya yadu a dandalin soshiyal midiya, inda ya nuna tsadaddiyar rayuwar jin dadi da wata mabaraciya ke yi.

Bidiyon ya nuno matar tana duba soyayyar kaza da dan tallan ke siyarsa, yayin da ta zauna a kasa kanta lullube da hijabi.

Mabaraciya ta darje ta siya soyayyar kaza
“Kasuwa Ta Yi Kyau”: Mabaraciya Ta Siya Soyayyar Kaza, Ta Darje Ta Zabi Wanda Take So Hoto: TikTok/@enycrown
Asali: TikTok

An gano matar tana ta zabo soyayyar kaza da aka yi wa yanka-yanka da cokali mai yatsu, kamar dai tana zabo wanda take so daga bokitin.

Kara karanta wannan

“Takun kudi”: Bidiyon diyar Dangote tana rawan kasaita ya dauka hankali

Mai tallan na ta kallo cike da mamaki yayin da mabaraciyar ke zabo wanda take so, kuma da alama bata ma san ana daukarta bidiyo ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon ya haddasa cece-kuce a tsakanin jama'a da suka cika da mamaki, da tambayar sahihancin barar da matar ke yi sannan suka zargeta da damfarar mutane.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a kan bidiyon mabaraciya da ke siyan kaza

Dotunmideta yi martani:

"Toh so ake kada ta ci abinci kuma?"

Folarin:

"Mabaraciyar abuja ne ke yin irin wannan rayuwar jin dadin."

Chioma Cynthia:

"Wa ya sani ko ta dade tana tara kudi saboda faruwar irin wannan rana, don Allah ku bari ta ji dadinta."

Brinn149:

"Daga karshe. Na ji dadin ganin wannan. Ashe suma suna da rana mai kyau."

Favour Felix:

"Kada marata su ci kaji kuma?"

Kara karanta wannan

So gamon jini: Daga yanke mata farce, kyakkyawar budurwa ta fada soyayya da mai yankan kumba

Arin63636:

"Tana da yancin jin dadin rayuwa wasu lokutan, koda kuwa sai ta yi bara kafin ta gamsar da kanta."

Ganyen ayaba ya samu matsayi

A wani labarin, mun ji cewa wata yar Najeriya mai wayo, Ọlaedo Chiọma Irene, ta yi murnar samun kudaden shiga daga sana'ar siyar da ganyen ayaba a kasashen waje, yayin da take Najeriya.

A wata wallafa da ta yi a shafin Facebook a ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, Chioma ta wallafa hotuna da ke nuna yadda take hada ganyenayaban a cikin ledoji da kwalaye bayan ta ninke su da kyau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng