Fitaccen Malamin Addini Ya Bayyana Mafita 1 Tak Ga Matsalolin Najeriya
- Fitaccen malamin addini, Bishop Matthew Kukah, ya magantu a kan matsalolin da suka addabi Najeriya
- Limamin cocin na Katolika ya ce duk wani dan Najeriya yana sane da matsalolin da kasar take fuskanta a halin da ake ciki
- Sai dai kuma, ya ce sai yan Najeriya da shugabanni masu kishin kasa sun hadu ne za a iya magance lamarin
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Bayelsa - Limamin cocin katolika na Sokoto, Bishop Matthew Kukah, ya ayyana cewar matsalolin Najeriya abu ne da za a iya shawo kansu.
Ya bayyana cewa duk dan Najeriya ya san matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu haka kuma mutane ne za su yi azamar magance matsalolin, rahoton Vanguard.
Wadanda suka jefa Najeriya a halin da take ciki basu tsira ba - Bishop Kukah
Kukah wanda ya yi jawabi a wajen wani taro da aka gudanar a Yenagoa, jihar Bayelsa a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba, ya bayyana cewa hatta ga wadanda suke da alhakin jefa Najeriya cikin matsaloli basu tsira ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin addinin wanda ya bayyana cewa ya samu damar haduwa da gaba daya shugabannin kasa da na mulkin soja a Najeriya baya ga Janar Sani Abacha, ya ce dukkaninsu suna da niyar bunkasa kasar amma sun gaza saboda rashin kudirin aiwatar da manufofinsu.
Hanya daya da za a warware matsalolin Najeriya
A cewarsa, kowace kasa a duniya tana da nata matsalolin kuma yan kasa da shugabanni masu kishi ne suke haduwa don magance irin wadannan matsaloli.
Ya bukaci yan Najeriya da su gano ainahin nasu gaskiyar domin samun ci gaba da kyau kamar yadda sauran kasashe suka yi.
Jaridar Daily Trust ta nakalto shi yana cewa:
"Abu mai kyau game da Najeriya shine cewa kowa ya san menene matsalolin da ke addabar kasar kuma mutane da ke da alhakin haddasa wadanan matsalolin suma basu tsira ba, suma basu san menene zaman lafiya ba.
"Yan Najeriya na magana kan sauran kasashe, ina tausayawa yan Najeriya da dama wadanda da kyar suke iya zuwa wuraren da ke makwabtaka da su saboda matsaloli da dama balle a kai ga zuwa sauran yankunan Afrika da sauran yankunan duniya.
"Koda dai, kowace kasa na da nata matsalolin, kalubalen da ke gabanmu a Najeriya shine cewa, me muke so, shin za mu iya samar da damokradiyya da ci gaban kasarmu? Tambaya ce mai wuyar amsa, domin abin da muke kira duniyar wayewa a yau ita ce shigowar shekaru 200 da aka yi Afrika wacce ta taimaka wajen gina wadannan kasashe.
“Don haka mu da kanmu muna tunanin, me ya sa ba mu zama kamar sauran mutane ba, ba mu zama kamar sauran ba ne saboda ya zama dole kowace kasa ta nemo nata gaskiyar don ci gaba. Ba wai ba za mu iya amfani da damokradiyya don ci gaban Najeriya ba, amma akwai wasu muhimman abubuwa da ya zama dole su kasance a kasa kafin mutane su fahimci damokradiyya.
"Har sai Najeriya ta magance matsalarta, za a dunga yi wa damokradiyya kallo kamar na caca."
Amurka ta gargadi yan kasarta a Najeriya
A wani labarin, mun ji cewa Amurka ta yi gagarumin gargadi ga yan kasarta da ke Najeriya, inda ta sanar da su hatsarin da ke tattare da wasu manyan otel-otel a manyan biranen kasar.
An saki wannan gargadi ne a matsayin karin bayani na gaggawa ga yan kasar Amurka a ranar Juma'a, 3 ga Nuwamba.
Asali: Legit.ng