Majalisar Sarakunan Arewa Sun Goyi Bayan Sarkin Hausawa da Aka Dakatar Kan Raina Olubadan Na Ibadan
- Al’ummar Hausawa mazauna garin Ibadan na Jihar Oyo sun shiga cikin rikicin shugabanci inda majalisar sarakunan gargajiya na Arewa a jihohin Kudu 17 suka marawa Sarkin Sasa Haruna Maiyasin baya
- Sarkin Hausawa na Ibadan, Alhaji Ali Zungeru ya dakatar da Maiyasin bisa zarginsa da rashin mutunta Olubadan na Ibadanland
- Sai dai, majalisar ta ce Zungeru ba shi da hurumin dakatar da Maiyasin don haka ta buƙaci Olubadan da ya sa baki domin hana tada zaune tsaye
Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
Ibadan, jihar Oyo - Al’ummar Hausawa mazauna Ibadan, babban birnin jihar Oyo, na ta fafatawa a rikicin shugabanci yayin da majalisar sarakunan gargajiya na Arewa a jihohin Kudu 17 suka marawa ɓangare ɗaya baya.
Majalisar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, a ranar Asabar, 4 ga watan Nuwamba, ta ce Sarkin Hausawa na Ibadan, Alhaji Ali Zungeru, ba shi da hurumin dakatar da Sarkin Sasa, Haruna Maiyasin daga muƙaminsa.
Me yasa aka dakatar da Sarkin Sasa?
Legit.ng ta tattaro cewa Zungeru ya dakatar da Maiyasin ne a ƙarshen wani taron al'ummar Hausawa da ya jagoranta kan rashin biyayya, rashin mutunta kujerar Olubadan na Ibadan da kuma bai wa jama’a muƙaman sarauta ba bisa ƙa'ida ba, ba tare da sahalewar Sarkin Hausawa na Ibadan ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, majalisar ta ce marigayi Olubadan na ƙasar Ibadan Oba Oloyede Asanike ne ya naɗa Maiyasin a shekarar 1983 kuma marigayi shugaban ƙasa, Janar Sani Abacha ya naɗa shi a matsayin shugaban majalisar sarakunan gargajiya na Arewa a shekarar 1994.
Bisa hakan, majalisar ta ce Maiyasin kawai yana ƙarƙashin shugabancin Olubadan na Ibadan ne, wanda yake yi wa biyayya.
"Sarkin Hausawa na Ibadan, Zungeru ba shi da ikon sauke Maiyasin saboda ba shi ne ya naɗa shi ba,” inji majalisar.
Majalisar Arewa ta buƙaci Olubadan da ya sa baki
Domin warware rikicin, majalisar ta buƙaci Olubadan na Ibadanland, Oba Balogun, da ya shiga tsakani ta hanyar yin tsawatarwa kan Zungeru da masu yi masa biyayya.
"Muna roƙon Olubaban na Ibadan, Oba Balogun da ya sanya baki ta hanyar tsawatarwa Zungeru da mabiyansa, domin ka da su sanya wasu ɓata gari su kawo tashin hankali musamman a Ibadan da jihar ba ki ɗaya."
"Sannan kuma a kauce wa saɓa doka da oda domin tashin hankali na ƙoƙarin tashi a tsakanin al'ummar Hausawa a jihar."
Masarauta Ta Tsige Babban Hakimi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Hakimin Ribadu da ke ƙaramar hukumar Fufore a jihar Adamawa, Alhaji Gidado Abubakar Aliyu, ya rasa muƙaminsa.
Hakimin ya rasa muƙaminsa ne bayan majalisar masarautar Adamawa ta tabbatar da tsige shi.
Asali: Legit.ng