FG Ta Yi Karin Bayani, Ta Fara Bincike Yayin da Jirgin Sama Dauke da Ministan Tinubu Ya Yi Hatsari
- Hukumar NSIB na binciken hatsarin jirgin sama da ya afku a filin jirgin saman Ibadan a ranar 3 ga watan Nuwamba, inda jirgin ya fado
- An tattaro cewa ba a rasarai ba yayin da NSIB ta tura masu bincike zuwa wurin da hatsarin ya faru
- Lamarin ya ritsa da wani jirgin sama kirar Flint Short Aero HS 125 da ke kan hanyar tafiya daga Abuja zuwa Ibadan kuma yana dauke da ministan wutar lantarki Adebayo Adelabu
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Hukumar Bincike ta Najeriya (NSIB) ta ce ta fara bincike kan hatsarin jirgin sama mai zaman kansa da ya afku a filin jirgin sama na Ibadan a raeen ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba.
An rahoto cewa a safiyar ranar Asabar, 4 ga watan Nuwamba, jami'an hukumar sun tabbatar da cewar jirgin ya fado, amma ba a rasa rai ba.
Sun bayyana cewa an tura masu bincike daga hukumar zuwa wajen da hatsarin ya afku, jaridar Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An nakalto kakakin hukumar ta NSIB, Tunji Oketumbi yana cewa:
"Eh, masu bincike na kasa a Ibadan. Za a sanar da karin bayani yayin da suke shigowa."
Shima daraktan hulda da jama’a da kare masu saye da sayarwa a NSIB James Odaudu ya tabbatar da faruwar hatsarin, rahoton Vanguard.
Legit Hausa ta tattaro cewa babban manajan hukumar kashe gobara ta jihar, Yemi Akinyinka, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.
Jirgin sama ya yi hatsari a Ibadan
A baya mun ji cewa wani jirgin sama mai zaman kansa ya tsallake rijiya da baya a filin jirgin saman Ibadan da ke Alakia a jihar Oyo.
Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, Jirgin saman wanda ya ɗauko fasinjoji ciki har da Ministan Bola Tinubu, ya kauce wa hanya yayin sauka a filin jirgin.
A rahoton jaridar Daily Trust, jirgin da ke dauke da Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi hatsari a kusa da filin jirgin sama na Ibadan a jihar Oyo yayin sauka.
Asali: Legit.ng