Wata Sabuwa: Masarautar Adamawa Ta Tsige Babban Hakimi Daga Karagar Mulki

Wata Sabuwa: Masarautar Adamawa Ta Tsige Babban Hakimi Daga Karagar Mulki

  • Masarautar Adamawa ta tuge rawanin hakimin Ribaɗu da ke ƙaramar hukumar Fufore, Alhaji Gidado Abubakar Aliyu
  • Basaraken ya rasa kujerarsa ta sarauta ne bayan masarautar ta dakatar da shi daga ofis tun a watan Afrilu, 2023
  • A wata wasiƙa da aka aika masa, masarautar ta ce an kori hakimin ne bisa amincewar gwamna Ahmadu Fintiri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Adamawa - Majalisar masarautar Adamawa ta tsige hakimin Ribadu da ke karamar hukumar Fufore Alhaji Gidado Abubakar Aliyu, daga kan karagar sarauta.

Wannan na ƙunshe ne a wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin Sakataren masarautar, Kabiru Bakari, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan nasarar ɗan majalisar tarayya daga Kaduna

Masarautar Adamawa.
Masarautar Jihar Adamawa Ta Tsige Hakimin Rubadu Daga Karagar Mulki Hoto: Adamawa palace
Asali: Facebook

Wasiƙar na ɗauke da adireshin hakimin Ribaɗu, ma'ana masarautar ta tura masa da saƙon matakin da ta ɗauka na warware rawaninsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wasiƙar matakin tuge Hakimin zai fara aiki ne nan take da zaran sakon ya isa ga wanda aka yi dominsa.

Wani sashin wasiƙar korar Hakimin ta ce:

"Masarautar Adamawa ta umarce ni da na rubuto maka wannan takarda domin sanar da kai cewa mai girma gwamnan jihar Adamawa (Ahmadu Umaru Fintiri) ya amince a tsige ka."
"Gwamna ya amince da ɗaukar matakin tuge maka rawanin Sarauta a wata wasiƙa da ya aiko mai lamba MCA/GHY/S 24/T/Vol.11.201 da kwanan watan 2 ga watan Nuwamba, 2023."
"Ana umartar ka da ka miƙa dukkan takardun aiki da ke hannunka wanda ya ƙunshi katin shaida ga muƙaddashin sakararen masarautar Adamawa."

Meyasa masarautar ta tsige hakimin Ribaɗu?

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da CoS na shugaban majalisar dokokin Adamawa, sun turo saƙo mai tada hankali

Idan zaku iya tuna wa masarautar ta dakatar da Hakimin Ribaɗu daga ofishinsa na Sarauta tun a watan Afrilu, 2023, a yanzu kuma ta kore shi gaba ɗaya.

Sai dai wasiƙar korar ba ta bayyana dalilin da ya sa majalisar Masarautar da sauke hakimin ba, kuma ba bu wani ƙarin bayani kan hakan a hukumance.

APC da LP sun yi rashin nasara a Kotu

A wani rahoton kuma Kotun ɗaukaka kara ta maida wa Amobi Ogah na LP kujerarsa ta mamban majalisar wakilan tarayya daga jihar Abiya.

Ta kuma rushe zaɓen ɗan majalisar Udenu/Igboeze, Denis Agbo na LP, inda ta umarci INEC ta canza zaɓe a mazabar cikin kwanaki 90.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262