Wani Ya Kashe Dan Uwansa a Bauchi Saboda Ya Gaji Babur Dinsa

Wani Ya Kashe Dan Uwansa a Bauchi Saboda Ya Gaji Babur Dinsa

  • Hukumar yan sanda ta bayyana cewa ta kama wani matashi dan shekaru 25, Yakubu Adamu a jihar Bauchi
  • Adamu ya kashe dan uwansa ta hanyar soka masa wuka domin ya gaje babur dinsa
  • Yanzu haka ana bincike kan lamarin kuma da zaran an kammala yan sanda zasu gurfanar da wanda ake zargi a gaban Kotu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Rundunar yan sanda a Bauchi ta kama Yakubu Adamu, wani mazaunin kauyen Kumbi da ke karamar hukumar Kirfi ta jihar kan zargin soke dan uwansa, Yayaji Abubakar, da niyan mallakar babur dinsa.

Kakakin yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya shiga yanayi, za a fitar da shi zuwa kasar waje neman lafiya

Wani ya kashe dan uwansa saboda mashin
Wani Ya Kashe Dan Uwansa a Bauchi Saboda Ya Gaji Babur Dinsa Hoto: Nigerian Tribune
Asali: UGC

Tun 2020 wanda ake zargi ya fara satar babur, yan sanda

Kamar yadda Wakil ya bayyana, wanda ake zargin ya fito karara ya nuna yana da hannu a laifin da ake tuhumarsa kuma ya ce ya fara satar babur tun a 2020.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adamu ya bayyana cewa ya fara ne a lokacin da ya hada kai da wani dan yankinsu Auwalu inda suka sace wani babur kirar Bajaj ja. Ya kuma ce sun siyar da ita a kan N70,000 sannan suka raba kudin a tsakaninsu.

Rundunar yan sandan ta bayyana cewa a yanzu haka a ana kan bincike kuma da zaran an kammala za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu, rahoton Vanguard.

Wani bangare na sanarwar ta ce:

"A ranar 3 ga watan Oktoba da misalin karfe 7:30 na yamma, Usman Mohammed, mai shekaru 38 daga kauyen Gorondo ta yankin Alkaleri, jihar Bauchi ya kai rahoton hedkwatar yan sanda da ke Kirfi. Ya bayyana cewa a wannan rana da misalin karfe 3:40 na yamma, Yakubu Adamu mai shekaru 25 daga kauyen Kumbi ta yankin Alkaleri ya yi amfani da wuka mai kaifi, ya farmaki kaninsa, Yayaji Abubakar mai shekaru 25 a wannan yankin. Yakubu ya yi masa fashin babur dinsa Bajaj ja mai lamba 526-OG, wanda ba a riga an yi masa kudi ba.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya magantu kan yadda aka lakada masa duka a jihar Imo

"Wanda ake zargin ya yi amfani da wuka mai kaifi wajen ji masa rauni da dama, wanda ya kai ga ya raunata shi a ciki da hannayensa. Da samun rahoton, nan take wata tawagar jami'ai ta shiga aiki da daukar wanda aka illata zuwa babban asibitin Alkaleri, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa. An kama wanda ya aika laifin kuma yanzu haka yana amsa tambayoyi a ofishin yan sanda."

Magidanci ya rasu wajen kare matarsa

A wani labarin, mun ji cewa wani matashin magidanci ɗan shekara 25 a duniya, Ibrahim Ahmadu, ya rasa rayuwarsa yayin ƙokarin ceton matarsa, Amina Sani, daga sharrin ƴan daba.

Leadership ta ruwaito cewa ƴan daban sun yi yuƙurin ƙwace masa mata, garin kare daraja da martabar matarsa suka kashe shi a kauyen Bazai, ƙaramar hukumar Shira a jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel