Hankula Sun Tashi Yayin Da Malamin Addini Ya Yi Batar-Dabo a Abuja

Hankula Sun Tashi Yayin Da Malamin Addini Ya Yi Batar-Dabo a Abuja

  • Malamin addini a majami'ar Archdioese ta Abuja, ya yi batar dabo tun a ranar 1 ga watan Oktoba, 2023, har yanzu ba a ganshi ba
  • Fada Samson ya bar gidansa a ranar da misalin karfe tara na dare, sai dai tun daga lokacin babu wanda ya kara jin duriyarsa ko sanin inda ya ke
  • Sai dai hukumar rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja (FCT), ta ce ba ta da masaniya kan batan malamin majami'ar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - An sanar da bacewar Rabaran Fada Samson Emokhidi, malamin majami'ar Archdioese ta Abuja.

A cewar sanarwar da majami'ar ta fitar, Samson ya bace ne a ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba, bayan da ya bar gidansa wajen misalin karfe tara na dare.

Kara karanta wannan

‘'Gwamnatin Tinubu za ta tsamo 'yan Najeriya miliyan 50 daga kangin talauci,’' Betta Edu

Samson Emokhidi
Malamin addinin ya bata ne tun bayan da ya bar gida a ranar 1 ga watan Oktoba, 2023 Hoto: Catholic Trend
Asali: Twitter

Sanarwar wacce shugaban majami'ar Archdiocese, Fada Sam Tumba ya sanya wa hannu, ta ce ba a kara jin duriyar malamin majami'ar ba tun bayan batansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majami'ar ya yi kira ga daukacin mambobin majami'ar tasu da su kasance masu sanya Fada Samson a cikin addu'i'on su, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majami'ar ta roki duk wani mai masaniya kan inda za a samu malamin majami'ar da ya tuntubi shugaban majami'ar kai tsaye.

"Muna sanar da daukacin mambobin majami'ar Arhdiocese cewa dan uwanmu kuma Fada Samson Emokhidi, wanda ya bar gidansa ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba, 2023, da misan karfe 9 na dare, an neme sa an rasa."
Ya bata ba tare da jin duriyarsa ba. Shugaban majami'ar ya bukaci mu kasance masu sanya malamin cikin addu'o'inmu, tare da tuntubarsa idan har an samu wani labari na inda ya ke.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun yi nasarar dakile mummunan harin Boko Haram a Kano, sun yi bayani

- A cewar sanarwar.

Tumba ya ce tuni suka sanar da hukuma batu kan batan malamin majami'ar, wadanda a cewar sa tuni suka fara bincike don gano inda ya ke.

Sai dai ko da aka tuntube ta a safiyar ranar Litinin, Josephine Adeh, jami'ar hulda da jama'a ta rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja (FCT), ta ce ba ta da masaniya kan wannan lamari.

Don girman Allah a dakatar da shirin BBNaija - Malamin coci ya roki FG

A wani labarin kuma, Ven. Ifeanyi Akunna, babban malamin cocin Epiphany da ke Abuja ya roki gwamnatin tarayya da ta dakatar da shirin Big Brother Nigeria (BBNaija) da sauran shirye shirye makamantansa.

BBNaija wani shiri ne da ake gabatarwa na rayuwar zahiri, inda mutanen cikin shirin ke killace a gida daya na tsawon wani lokaci, kuma ana bayar da kyautar makudan kudade.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.