Cin Zarafi: Kungiyar NLC Ta Fadi Ranar Tsunduma Yajin Aiki, Ta Tura Bukatu 6 Ga Gwamnati
- Kungiyar Kwadaga ta NLC ta ayyana Laraba 8 ga watan Nuwamba a matsayin ranar tsunduma yajin aikin gama-gari
- Kungiyar ta fitar da wannan sanarwa ce a yau Juma’a 3 ga watan Nuwamba a Abuja kan cin zarafin Joe Ajaero
- Har ila yau, kungiyar ta tura bukatu ga gwamnati har guda shiga wanda idan ba ta aiwatar da su ba za su tsunduma yajin aikin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Kungiyoyin Kwadagon NLC da TUC sun saka ranar da za su tsunduma yajin aikin gama-gari a Najeriya.
Kungiyar ta ce za ta shiga yajin aikin gama-gari a ranar Laraba 8 ga watan Nuwamba kan cin zarafin shugabansu, Joe Ajaero da aka yi.
Wane gargadi NLC ta yii ga gwamnati?
NLC ta bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a yau Juma’a 3 ga watan Nuwamba a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, kungiyar ta mika wa gwamnatin bukatunta guda shida da su ka hada da cire kwamishinan ‘yan sanda a jihar Imo, cewar Punch.
Sauran sun hada da sauke dukkan kwamnadojin yanki na rundunar da wasu masu mukamai kan cin zarafin Ajaero da wasu ma’aikata.
Mene dalilin kama shugaban NLC?
Legit Hausa ta ruwaito cewa a ranar Laraba 1 ga watan Nuwamba jami'an 'yan sanda sun cafke shugaban NLC, Joe Ajaero a Owerri da ke jihar Imo.
'Yan sandan sun kwamushe shi ne yayin gudanar da zanga-zanga a sakatariyar kungiyar kan wasu korafe-korafen ma'aikata.
Kungiyar daga bisani ta gargadi gwamnati da ta sake shugaban nasu ko kuma su tsunduma yajin aiki, cewar Vanguard.
Jami'an tsaro sun cafke shugaban NCL, Ajaero
A wani labarin, jami'an 'yan sanda a jihar Imo sun cafke shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Joe Ajaero a birnin Owerri.
'Yan sandan sun kama Ajaero ne yayin gudanar da wata zanga-zanga a sakatariyar kungiyar da ke birnin a ranar Laraba 1 ga watan Nuwamba.
Wannan na zuwa ne yayin da kungiyar ke takun saka da gwamnati kan inganta rayuwar al'ummar kasar.
Asali: Legit.ng