"Gobe Jumu'a" Shugaban Majalisar Wakilai Abbas Ya Yi Bayani Kan Ƙarin Ƙasafin Kuɗin.2023
- Shugaban majalisar wakilan tarayya ya ce mai yiwuwa shugaba Tinubu ya rattaɓa hannu kan karin kasafin kuɗin 2023
- Tajudeen Abbas ya bayyana haka ne bayan majalisun tarayya sun amince da karin kasafin ya zam doka bayan tsallake karatu na uku
- Bola Tinubu ya ce wannan ƙarin kasafin na kunshe da kuɗin tabbatar da tsaron ƙasa, da tallafin talakawa
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tajudeen Abbas, kakakin majalisar wakilai ta ƙasa, ya ce da yiwuwar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rattaba hannu kan karin kasafin kudin 2023 ranar Juma’a.
Abbas ya bayyana haka ne ranar Alhamis bayan kudirin ƙarin kasafin kuɗin wanda ya kai N2.17tr ya tsallake karatu na uku a majalisar dattawa da majalisar wakilai.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai karin kasafin ya tsallake karatu na daya da na biyu a majalisar dattawa da ta wakilai, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun da fari dai, Shugaba Bola Tinubu ya bukaci ‘yan majalisar da su gaggauta amincewa da kudirin ƙarin kasafin kuɗin saboda muhimmancinsa.
Kafin amincewa da kasafin a ranar Alhamis, sai da majalisar ta tafi hutu na ɗan loƙacin kafin daga bisani ta gaggauta dawowa aka kaɗa kuri'ar amince wa da shi.
Dalilin da yasa aka yi saurin amincewa da kasafin
Da yake jawabi kan ci gaban, shugaban majalisar ya ce sun yi haka ne saboda shugaban "zai iya" sanya hannu kan kasafin ya zama doka gobe Juma'a.
Abbas ya ce:
“Abin da muka yi tun da farko shi ne tsarin da muka saba na jira har zuwa ranar da za a kaɗa kuri'a da kuma zartar da shi ya zama doka.
Tun a ranar Litinkn ɗin farkon wannan makon, majalisar zartarwa karƙashin Bola Ahmed Tinubu ta amince da ƙarin N2.17tr a kasafin kuɗin shekarar 2023, Channels tv ta tattaro.
Gwamnan Imo ya karya shiru kan abinda ya faru
A wani rahoton kuma Gwamna Hope Uzodinma ya yi magana kan tsautsayin da ya faru har shugaban NLC na ƙasa ya sha wahala a jihar Imo.
Jim kaɗan bayan Bola Tinubu ya miƙa masa tutar APC a Villa, gwamnan ya zargi Joe Ajaero da tsoma hannu a siyasar jihar.
Asali: Legit.ng