Majalisa Ta Yi Watsi Da Siyan Jirgin Ruwan Shugaban Kasa Na N5bn Daga Kasafin Kudi

Majalisa Ta Yi Watsi Da Siyan Jirgin Ruwan Shugaban Kasa Na N5bn Daga Kasafin Kudi

Abubakar Bichi, shugaban kwamitin dai daito na kasafin kudi na majalisar wakilan tarayya yace sun karkatar da kudin da aka ware domin sayawa shugaban kasa jirgin ruwa na alfarma zuwa ga kasafin kudin tallafawa dalibai da bashi.

Bichi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan rattaba hannu kan kasafin kudin karo na biyu, jaridar The Cable ta ruwaito.

"A iya sani na a yanzu, babu sauran batu kan wani jirgin ruwa na shugaban kasa. Mun kara kudin a kasafin kudin tallafawa dalibai da bashi," a cewarsa.

Idan za ku iya tunawa, da farko an sanya kasafin kudin tallafawa daliban akan N5bn, sai dai yanzu mun kara shi zuwa N10bn.

- Abubakar Bichi

Cikakken labarin yana zuwa...

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.