Shugaban NLC Ya Shiga Yanayi, Za a Fitar da Shi Zuwa Kasar Waje Neman Lafiya

Shugaban NLC Ya Shiga Yanayi, Za a Fitar da Shi Zuwa Kasar Waje Neman Lafiya

  • Raunukan da shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Kwamrad Joe Ajaero ya ji sun kara girmama fiye da yadda aka yi tsammani
  • An rahoto cewa za a fita da Ajaero kasar waje domin yin magani sakamakon raunukan da ya samu a hatsaniyar da ya faru a jihar Imo
  • Yan sanda sun kama shugaban NLC din a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba sannan daga bisani aka sake shi dauke da kumburarren fuska

Jihar Imo - Rahotanni sun kawo cewa ana shirin fita da shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC) Kwamrad Joe Ajaero kasar waje domin neman lafiya kan raunukan da ya samu yayin wani rikici da ya barke a jihar Imo, rahoton Blueprint.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, sakataren labaran NLC, Benson Upah, ya ce an kasa kula da Ajaero a asibitin FMC Owerri saboda yanayin raunukan da ya ji a yayin hargitsin.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya magantu kan yadda aka lakada masa duka a jihar Imo

Za a fitar da shugaban NLC waje
Shugaban NLC Ya Shiga Yanayi, Za a Fitar da Shi Zuwa Kasar Waje Neman Lafiya Hoto: @firstladyship
Asali: Twitter

A ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba ne shugaban na NLC ya tara ma'aikatan Imo domin yin zanga-zanga a jihar kan zargin take yanci da cin zarafin ma’aikata da gwamnatin jihar ta yi.

Sai dai kuma, zanga-zangar lumanan da aka shirya ya zama rikici bayan wasu yan daba sun farmaki masu zanga-zangar da shugabannin kwadagon.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban NLC ya fadi halin da ya shiga yayin da aka kama shi a Imo

Da farko Legit Hausa ta rahoto cewa Ajaero ya bayyana halin da ya shiga yayin da aka kama shi a Owerri, babban birnin jihar Imo.

Shugaban na NLC ya ce an lakada masa duka kuma cewa lallai Ubangiji ya dauki lokaci wajen halitarsa tun da har ya rayu daga halin da ya shiga.

Ajaero ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafofin watsa labarai a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da aka kwashi shugaban NLC Ajaero zuwa asibiti, cikakken bayani

An kwashi Ajaero zuwa asibiti

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa an kwantar da shugaban kungiyar kwadago na kasa, Kwamrad Joe Ajaero a wani asibiti a garin Owerri, jihar Imo.

"An ci zarafinsa sosai, idonsa na dama a rufe yake ruf a daidai lokacin da aka ji daga gare shi," kamar yadda kakakin kungiyar kwadagon, Kwamrad Benson Upah, ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng