Kwankwaso Ne Dalilin Da Ya Sa Alkali, Hunkuyi Suka Koma APC – Jigon NNPP
- Jam'iyyar NNPP ta bayyana dalilin da yasa tsohon shugabanta, da wasu 'yan takarar gwamna karkashinta suka sauya sheka zuwa APC
- NNPP na ganin nuna kaka-gida da son mamaye ragamar jam'iyyar da Kwankwaso ke yi, yasa jiga-jigan jam'iyyar ke ficewa daga jam'iyyar
- Jam'iyyar NNPP dai na ci gaba da fuskantar rikice-rikicen cikin gida, inda har a baya-bayan nan wani tsagi na jam'iyyar ya dakatar da Kwankwaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Wani tsagi na jam'iyyar NNPP da ke goyon bayan uban jam'iyyar, Chief Boniface Aniebonam sun bayyana cewa tsohon shugaban jam'iyyar na kasa, Farfesa Ahmed Alkali da 'yan takarar gwamnan jihar Kaduna da na Benue a karkashin jam'iyyar, sun bar jam'iyar ne sakamakon kaka-gida da sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi.
Farfesa Alkali, wanda ya ajiye mukamin shugabancin jam'iyyar a watan Maris, ya fice daga jam'iyyar a watan Satumba. Ya kuma jagoranci 'yan takarar gwamnoni na jam'iyyar zuwa APC, The Nation ta ruwaito.
A cikin wata sanarwa daga sakataren watsa labarai na tsagin Aniebonam, Alhaji Abdulsalam Abdulrasaq, jam'iyyar ta kuma alakanta sauyin shekar da makarkashiyar Kwankwaso na son mamayewa tare da kwace ragamar jam'iyyar gaba daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin da sanarwar ke nuna sauya shekarar tsohon shugaban jam'iyyar da sauran, a matsayin abu mai ciwo, sanarwar ta kuma bayyana su a matsayin jajurtatun 'yan kasa, wadanda ba za su iya zama a inda ba a san mutuncin dan Adam ba.
Abinda sanarwar ke cewa game da sauyin shekar Farfesa Ali da su Hukuyi
Sanarwar ta bayyana cewa:
Farfesa Rufai Ahmed Alkali, Farfesa Bem Angwe, sanata Othman Hunkuyi da sauransu, sun fice daga NNPP ne sakamakon kaka-gida da kuma son zuciya, na nuna mamaya da kwace ragamar jam'iyyar da Dr Bonfice O Aniebonam ya kafa, da kuma kungiyarsa ta NAGAFF.
Idan ba a manta ba, Farfesa Bem Angwe da sanata Suleiman Othman Hunkuri, sun yi yarjejeniya tsakaninsu da Rabiu Musa Kwankwaso da jam'iyyar NNPP wanda ta kai ga anyi hadakar kungiyoyin Kwankwasiyya da na TNM.
Haka zalika, Farfesa Rufai Alkali ya bar mukaminsa na shugabanci tare da ficewa daga jam'iyyar sakamakon nuna kaka-gida da Kwankwaso ya yi, da kuma muradin son mallake NNPP, ba tare da kallon halascin da aka yi masa na yin takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar ba.
Hatta 'yan takarar gwamna karkashin jam'iyyar, an yi watsi da duk wata jarjejeniya da aka kulla da su, yayin da Kwankwaso ke kulla makarkashiya da son ganin ya yi handama da baba-kere, lamarin da ya sa suka hakura da jam'iyyar ganin lamarin yaki ci yaki cinyewa.
Sannan, kowa ya nuna rashin jin dadinsa na yadda za a ce a dakatar da uba, kuma wanda ya samar da jam'iyyar daga wannan tafiya, kowa ya nuna kuskuren Kwankwaso, amma ya yi biris da ra'ayin kowa.
- A cewar sanarwar.
Haka zalika sanarwa ta yi nuni da cewa tuni jam'iyyar ta hasasho zuwan irin wannan ranar da mambobinta za su rinka ficewa zuwa wata jam'iyyar sakamakon nuna iko da Kwankwaso ke yi, da kuma rashin girmama su da ra'ayoyin su.
Sanarwar ta kuma yi masu fatan alkairi, tare da cewar, "kofarmu a bude take a kowanne lokaci, idan suka bukaci dawowa, kasancewar yanzu jam'iyyar ta dauki mikati na yin garanbawul da kawo sabbin tsare tsare da za su amfani kowa."
NNPP Ta Rusa Kwamitin NWC Karkashin Abba Kawu Ali, Ta Amince Da Korar Kwankwaso
Kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta amince da rushe kwamitin ayyuka na NWC karkashin jagorancin Abba Kawu Ali.
Kwamitin BoT ta kuma tabbatar da korar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabi'u Musa Kwakwanso, Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng