“Ya Ban Ga Kowa Ba a 2go?” Dan Najeriya da Ya Shafe Shekaru 15 a Yari Ya Yi Tambaya Mai Ban Dariya
- Wani dan Najeriya wanda ya fito daga gidan yari kwanan nan ya tambayi wani abokinsa dalilin da yasa bai ga mutane a manhajar 2go ba
- An tattaro cewa mutumin ya shafe shekaru 15 a gidan yarin, kasancewar tun a 2008 aka garkame shi har zuwa 2023
- 2go wani dandali ne na sada zumunta wanda ya shahara a shekarun baya, kuma mutumin ya yi tunanin har yanzu yana nan da farin jininsa a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wani dan Najeriya wanda ya shafe tsawon shekaru 15 a gidan yari ya dawo, kuma ya yi wata tambaya mai ban dariya.
A wani dan gajeren bidiyo da aka wallafa a TikTok, mutumin ya tambayi abokinsa dalilin da yasa babu kowa a dandalin 2go.
2go ya kasance dandalin sada zumunta mai matukar farin jini a tsakanin mutanen Najeriya a shekarun baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kan yi amfani da manhajar ne wajen tura sakonni cikin sauri, kuma matasan yan Najeriya da suka mallaki wayoyi masu intanet suna jin dadinsa sosai.
Yan Najeriya sun tuna da manhajar 2go
Sai dai kuma da tafiya ta yi tafiya, farin jinin da dandalin ke da shi ya dakushe. Wadanda suka tuna shi sun garzaya sashin sharhi don tuna baya.
An yi wa bidiyon take da:
"Wannan abokin nawa da ya tafi gidan yari tun 2008 ya dawo a makon jiya sannan ya tambayeni: 'me yasa kowa baya kan 2go?"
Shafin @kayhandsome5 ne ya wallafa bidiyon, wanda ya ce mutumin da aka saka daga gidan yari abokinsa ne.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani kan bidiyon mutumin da aka sako daga yari
@pytrhema ta ce:
"Dan uwa, ni ban ma yi amfani da 2go ba mahaifiyata tana da tsauri sosai bata bari na yi amfani da waya ba."
@Benita ta ce:
"Ni ban ma yi amfani da 2go ba saboda shekaruna 15 lokacin a SS1 lokacin da na fara jinsa ba tare da waya ba."
@OLALEKAN ya ce:
"Idan suka cire shekaru 15 daga shekarunsa me zai rage?"
@fesolola:
"Na san shi. Makarantar sakandare daya muka yi."
@hamzat abiodun ya ce:
"Ko jiya na shiga 2go dina. Har yanzu taurarona na "ultimate."
An siyarwa matashi teba a madadin waya
A wani labari na daban, wani bidiyo ya yadu a soshiyal midiya wanda ke nuna wani mutum cike da nadamar zuwa siyan wayar iPhone 15 a kasuwar 'Computer Village.
Bayan ya siya wayar iPhone, ya bude kwalin kawai sai ya ga teba nade a cikin kwalin don sa shi ya yi nauyi kamar da gaske akwai abu a ciki.
Asali: Legit.ng