FUG: Ɗalibai Mata Na Jami'ar Arewa da Aka Ceto Daga Hannun Ƴan Bindiga Sun Samu Tallafi Mai Tsoka
- Gwamnatin tarayya ta raba tallafin kuɗi ga ɗalibai mata na jami'ar tarayya da ke Gusau waɗan da aka ceto daga hannun ƴan bindiga
- Kwamishinan jin kai da harkokin rage raɗaɗi na Zamfara, Salisu Musa, ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Talata
- Wannan na zuwa ne bayan ministar jin ƙai da yaye talauci, Dokta Betta Edu, ta kai ziyarar kwana ɗaya jihar Zamfara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Dalibai mata na Jami’ar Tarayya ta Gusau (FUGUS) da aka ceto daga hannun ƴan bindiga sun samu tallafin kudi daga gwamnatin tarayya.
Kwamishinan jin ƙai da harkokin rage raɗaɗi na jihar Zamfara, Salisu Musa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Gusau, ranar Talata, Premium Times ta ruwaito.
Sanarwan mai ɗauke da sa hannun kakakin ma'aikatar jin ƙai ta jihar, Bashir Kabir, kwamishinan ya ce tallafin ya isa hannun ɗaliban da lamarin ya shafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Musa ya ce:
“Kowane daya daga cikin daliban mata guda 14 ta karbi tallafin makudan kuɗi N214,285 daga Gwamnatin Tarayya."
"A madadin gwamnatin jihar Zamfara, muna godiya da wannan karimci da kuma minista, Dokta Betta Edu, bisa wannan taimakon da ta baiwa daliban."
Zamfara zata haɗa kai da FG
Kwamishinan ya kuma bayyana kudirin gwamnatin jihar Zamfara na hada kai da gwamnatin tarayya wajen ceto mutanen da wannan matsala ta shafa a jihar da ke Arewa maso Yamma.
Ya yaba wa mahukuntan jami’ar da iyayen wadanda aka sace bisa hakuri da fahimtar juna, goyon baya da hadin kan da suka bayar a wannan lokacin mai cike da tashin hankali.
Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rawaito cewa ministar jin ƙai da kawar da talauci ta kai ziyarar aiki ta kwana daya a jihar inda ta jajantawa jami’ar da wadanda abin ya shafa.
Idan baku manta ba, ƴan bindiga sun shiga ɗakunan ɗalibai mata na jami'ar FUG, inda suka tafi da adadi mai yawa amma daga bisani dakarun soji suka yi nasarar ceto wasu., PM News ta ruwaito.
Sanata Natasha ta caccaki Yahaya Bello
A wani rahoton kuma Zababbiyar Sanatar Kogi ta tsakiya ta zargi gwamna Yahaya Bello da shirya maƙarƙashiyar kashe ta a lokacin zaɓe a watan Maris.
Natasha Akpoti-Uduaghan ta kuma maida martani kan kalaman da gwamnan ya yi bayan ta samu nasara a Kotun ɗaukaka ƙara.
Asali: Legit.ng