Mummunan Hatsarin Mota Ya Salwantar da Rayukan Mutum 12 a Jihar Zamfara

Mummunan Hatsarin Mota Ya Salwantar da Rayukan Mutum 12 a Jihar Zamfara

  • Rayukan mutum 12 sun salwanta a wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da su a jihar Zamfara
  • Hatsarin motan ya ritsa ne da wata motar bas tare da wata babbar mota ƙirar Toyyota Canter a kan titin Funtua-Gusau
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa hatsarin ya auku ne sakamakon ƙwacewa da motar bas ɗin ta yi wa direbanta saboda gudun da yake yi a titin

Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Jihar Zamfara - Akalla mutum 12 ne ciki har da ƙananan yara guda biyu suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya auku a ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara.

Hatsarin dai kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto ya auku ne a ƙauyen Kucheri da ke kan titin Funtua-Tsafe a karamar hukumar Tsafe da misalin karfe 1:20 na rana a ranar Talata, 31 ga watan Oktoban 2023.

Kara karanta wannan

Bam ya tashi da masu zuwa jana'iza, mutane sama da 20 sun mutu a jihar Yobe

Mutum 12 sun rasu a hatsarin mota
Hoton wani hatsarin mota (ba inda abin ya auku ba) Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Hatsarin ya shafi mutum 24, mutum 22 na tafiya ne a cikin wata motar bas , yayin da sauran biyun ke cikin wata mota ƙirar Toyota Canter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda hatsarin motar ya auku

Wani Shaidar gani da ido ya bayyana cewa, motar bas ɗin ta ƙwacewa direbanta, inda ya afkawa motar Toyota da ke tahowa, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwar fasinjoji 12 a cikin motar.

Shaidan ya ƙara da cewa an kwantar da wasu fasinjoji da dama, wadanda suka samu raunuka daban-daban a babban asibitin Tsafe.

A kalamansa:

"Direban motar bas ɗin da ya taho daga Funtua ya kasa sarrafa motar bayan ta ƙwace masa, inda ya afkawa babbar motar da ke tahowa daga yankin Tsafe. Yawancin mutanen da hatsarin ya shafa nan take suka rasu a wajen."

Menene ya haddasa hatsarin motar?

Kara karanta wannan

Rayukan mutum 3 sun salwanta a wani kazamin hatsarin mota a jihar Legas

Wani jami'in hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC), wanda baya son a bayyana sunansa saboda ba shi da izinin yin magana da manema labarai, ya ce hatsarin ya auku ne sakamakon tuƙin ganganci da wuce gona da iri

"Ina cikin jami'an FRSC da suka gudanar da aikin ceto a wurin da hatsarin ya auku. Waɗanda suka rasa rayukansu a hatsarin sun haɗa da manyan mutane guda 10 da yara ƙanana gida biyu." A cewarsa.

Rayukan Mutum Uku Sun Salwanta a Legas

A wani labarin kuma, rayukan mutum uku sun salwanta bayan wata mota banke mutane a jihar Legas.

A cikin mutanen da suka rasa ransu har da wata tsohuwa mai shekara 72 a duniya a hatsarin da ya auku kusa da tashar motar Gbagada a birnin Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng