Shugaba Tinubu Ya Aika Sako Majalisa, Ya Buƙaci Ta Amince da Ƙarin Kasafin 2023 da Wani Abu 1
- Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar wakilan tarayya ta amince da N2.1tr a mataayin ƙarin kasafin kuɗin shekarar 2023
- Shugaban ƙasar ya aike da sakon wannan bukata ne a wata wasiƙa da ya miƙa wa majalisar ranar Talata, 31 ga watan Oktoba
- Ranar Litini, Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren ƙasa, Atiku Bagudu, ya ce za a yi amfani da ƙarin kasafin a fannin tsaro da sauransu
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rubuta wasiƙa zuwa majalisar wakilan tarayya kan sabon ƙarin kasafin kuɗi na shekarar 2023.
Channels tv ta tattaro cewa a sakon da ya tura, shugaba Tinubu ya buƙaci majalisar wakilan tarayyan ta amince da N2,176,791,286,033 a matsayin ƙarin kasafin 2023.
Ya yi bayanin cewa a za a yi amfani da wannan ƙarin kasafin wajen cike gurbin ƙarin albashin da aka yi wa ma'aikatan tarayya, tsaro da sauransu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙasar ya kuma aike da daftarin tsarin rage yawan kashe-kashen kuɗi da dabaru na tsakanin 2024-2026 ga majalisar wakilan tarayya.
FEC ta amince da ƙarin kasafi karo na biyu
Idan baku manta ba a ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba, 2023, majalisar zartarwa (FEC) ta amince da N2.1tr a matsayin ƙarin kasafin shekarar 2023.
Da yake jawabi bayan taron FEC a Abuja, Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Atiku Bagudu, ya ce an yi ƙarin kasafin kudin ne don magance batutuwan gaggawa.
"Majalisar ta yi duba tare da la'akari da bukatar karin kasafi karo na biyu a shekarar 2023," in ji shi a fadar gwamnati da ke Abuja, The Nation ta ruwaito.
Shugaba Tinubu ya amince da ƙarin Naira tiriliyan 2.18 a kasafin kuɗin 2023, ya faɗi ayyukan da za a yi
"Daga nan aka amince da N2,176,791,286,033 a matsayin karin kasafin kudin, kuma wannan karin kasafin kudin za a yi amfani da shi a harkoki gaggawa da suka hada da Naira biliyan 605 na tsaron kasa."
Ministan ya bayyana cewa ƙarin kasafin ya kunshi kuɗin da za a cike gurbin ƙarin albashin da aka yi wa ma'aikata da kuɗin da FG zata raba wa magidanta don rage radaɗi.
APC ta ƙara rikita PDP
A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC ta ƙara yi wa jam'iyyar PDP babban lahani yayin da zaɓen gwamna ke ƙara kusantowa a jihar Kogi.
Tsohon ɗan takarar gwamna a inuwar PDP da magoya bayansa, mambobin jam'iyyu uku sun sauya sheka zuwa APC.
Asali: Legit.ng