Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ƙarin N2.18tr a Kasafin Kuɗin 2023, Ya Faɗi Ayyukan da Za a Yi

Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ƙarin N2.18tr a Kasafin Kuɗin 2023, Ya Faɗi Ayyukan da Za a Yi

  • Gwamnatin tarayya ta amince da ƙarin N2.176tr a matsayin ƙarin kasafin kuɗin shekarar 2023
  • Majalisar zartarwa ƙarƙashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ce ta amince da haka yayin zaman ranar Litinin 30 ga watan Oktoba, 2023
  • Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu, ya lissafo ayyukan da za a yi da kuɗin kafin karewar 2023, mun tsakuro muku wasu daga ciki

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) ta amince da ware maƙudan kuɗi da suka kai N2,176,791,286,033 a matsayin karin kasafin kuɗin 2023 karo na biyu.

zaman majalisar zartarwa ta tarayya a Villa.
FEC Ta Amince Da Karin N2.1tr a Kasafin Kudin da Buhari Ya Yi Na Karshe Hoto: Presidency
Asali: UGC

Ministan kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Alhaji Atiku Bagudu ne ya bayyana haka yayin hira da ƴan jarida jim kaɗan bayan fitowa daga taron FEC a fadar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya faɗi ƙungiyoyin 'yan ta'adda 2 da ke barazanar shafe Najeriya

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranci taron na yau Litinin a Aso Villa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwan da za a yi da ƙarin kasafin

Ministan ya ce ƙunshin ƙarin kasafin, wanda za a tura wa majalisar tarayya, za a yi amfani da shi wajen ɗaukar nauyin batutuwan gaggawa.

Daga ciki, Bagudu ya ce an ware Naira biliyan 605 domin ƙara inganta tsaron ƙasa da kwanciyar hankalin al'umma, rahoton The Nation ya tattaro.

A cewarsa, "An ware wannan kuɗi don dorewar nasarorin da aka samu a sha'anin tsaro kuma wadannan kudade ne da hukumomin tsaro ke bukata kafin shekara ta kare."

Ministan ya ce an kuma ware Naira biliyan 300 na gyaran gadoji da kuma gyara, sake gina wa da kuma tsare manyan tituna a faɗin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Ma'aikata sun garƙame majalisar dokokin jihar Kano, bayanai sun fito

Bayan haka, Atiku Bagudu ya yi bayanin cewa FG ta ware wasu biliyan 210 domin biyan ƙarin albashin ma'aikata na wucin gadi N35,000 tsawon watanni shida.

Ya kuma tunatar da cewa gwamnatin tarayya ta amince zata biya kowane ma'aikacinta ƙarin N35,000 yayin tattauna wa da ƙungiyoyin kwadugo NLC da TUC.

Haka zalika an ware biliyan 400 da za tura wa ƴan Najeriya magidanta domin rage masu raɗaɗin zare tallafin man fetur.

Gwamna Fubara na ganawa da dattawan PDP

A wani rahoton na daban kuma Gwamnan jihar Ribas ya shiga taro da manyan ƙusoshin jam'iyyarnPDP a gidansa na gidan gwamnati da ke Patakwal.

Wannan gana wa na zuwa ne yayin da wasu ƴan majalisar dokokin jihar suka fara yunkurin sauke shi daga kan kujerar gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel