Yajin aiki: Ma'aikata Sun Garƙame Majalisar Dokokin Jihar Kano, Bayanai Sun Fito
- Ma'aikatan sun tsunduma yajin aiki, sun rufe zauren majalisar dokokin jihar Kano ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba, 2023
- Shugaban ƙungiyar ma'aikatan majalisar dokokin reshen Kano, ya ce ba zasu janye wannan yajin aiki ba sai an biya masu buƙatunsu
- A cewarsa, tun shekaru biyu da suka wuce Buhari ya sa hannu a dokar bai wa majalisun dokokin damar cin gashin kansu, amma an ƙi aiwatarwa
Ahmad Yusuf, Editan Legit Hausa ya shafe shekaru yana kawo rahotanni kan al'amuran siyasa da harkokin yau da kullum
Jihar Kano - Mambobin ƙungiyar ma'aikatan majalisar dokoki ta Najeriya (PASAN) reshen jihar Kano, sun garƙame zauren majalisar dokokin jihar Kano ranar Litinin.
Ma'aikatan sun ɗauki wannan mataki ne yayin da suka bi sahu, suka tunduma yajin aikin sai baba ta gani, wanda ƙungiyarsu ta ƙasa ta ayyana shiga a faɗin Najeriya.
Shugaba Tinubu ya amince da ƙarin Naira tiriliyan 2.18 a kasafin kuɗin 2023, ya faɗi ayyukan da za a yi
Shugaban PASAN na jihar Kano, Bashir Yahaya, shi ne ya tabbatar da rufe majalisar dokokin ranar Litinin yayin hira da ƴan jarida, kamar yadda Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin fara yajin aiki
"Eh haka ne, mun bi sahu wajen shiga yajin aiki kamar yadda shugaban ƙungiyar mu na ƙasa ya bada umarni."
"Wannan yajin aiki ya biyo bayan ƙarewar wa'adin da ƙungiyar mu ta bai wa gwamnati na aiwatar da tsarin cin gashin kai ga ɓangaren majalisar dokoki."
- Bashir Yahaya.
Ya ƙara da bayanin cewa yajin aikin ya samo asali ne sakamakon gazawar gwamnatin jihar wajen aiwatar da ‘yancin cin gashin kai kan harkokin kudi ga bangaren majalisa.
“Kungiyar ta yi hakuri na tsawon shekaru biyu bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar cin gashin kan majalisa, amma gwamnonin jihohi sun gaza aiwatar wa."
Yaushe za su gama yajin aikin?
Shugaban PASAN na Kano ya ci gaba da cewa ƙungiyar zata ci gaba da wannan yajin aiki har sai an biya masu buƙatunsu.
Yahaya ya ƙara da bayyana cewa majalisar dokokin jihar Kano za ta ci gaba da zama a rufe har sai an samu sabon umarnin da ya saɓa wa haka daga ƙungiya ta ƙasa.
An zaɓi sabon kakakin majalisa a Ribas
A wani rahoton kuma Mambobin majalisar dokokin jihar Ribas da ke goyon bayan gwamna Fubara sun zaɓi sabon shugaban majalisar dokoki.
Wannan ci gaban na zuwa ne yayin da majalisar ta fara yunƙurin.tsige Fubara daga kan mulkin jihar Ribas ranar Litinin.
Asali: Legit.ng