Wike: Tsohon Minista Ya Zazzagawa Ahmad Gumi Masifa Saboda Ya Taba Ministan Abuja
- Femi Fani-Kayode ya bi sahun wadanda su ke caccakar Ahmad Abubakar Mahmud Gumi a kan wasu magangangu da ya yi
- Tsohon Ministan tarayyan ya yi rubutu ya na mai yin Allah-wadai da sukar da malamin musuluncin ya yi wa Ministan birnin Abuja
- ‘Dan siyasar ya ce abin da Sheikh Gumi ya fada game da Nyesom Wike za su iya harzuka jama’a har a barke da rigima a kasar nan
M. Malumfashi ya yi shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Femi Fani-Kayode wanda ya yi Minista a gwamnatin Najeriya, ya gargadi Ahmad Abubakar Mahmud Gumi game da wasu kalamansa.
A wani zungureren rubutu da ya yi a shafin Vanguard, Cif Femi Fani-Kayode ya zargi Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi da neman tada rikici.
‘Dan siyasar ya ce kalaman malamin addinin za sui ya kawo tarzoma da tashin-tashina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Femi Fani-Kayode v Dr. Ahmad Gumi
A dalilin haka, Fani-Kayode ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta ja hankalin Dr. Ahmad Gumi, ya na kuma mai yabawa wasu manyan Arewa.
Dattawan yankin Arewa da su ka nesanta kan su daga kalaman Ahmad Gumi sun yi daidai a cewar jigon na jam’iyyar APC a Kudancin Najeriya.
Me Sheikh Gumi ya fada a kan Wike?
Da yake wani karatu a masallacin Sultan Bello da ke garin Kaduna kwanakin baya, Ahmad Gumi ya yi kaca-kaca da sabon Ministan birnin Abuja.
Shehin malamin ya zargi Nyesom Wike da kokarin ganin bayan Musulmai, kuma ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da murkushe mutanen Arewa.
Martanin Femi Fani-Kayode
"Duk yadda ka duba labarin, abu guda ne yake a zahiri; Gumi ya na kokarin jawo rikicin addini da na kabilanci a Najeriya
Kuma ana bukatar wani ya dawo da shi cikin taitayinsa kafin a makara."
- Femi Fani-Kayode
A rubutun da ya yi mai tsawon shafi biyu a jaridar, ‘dan siyasar da ya shahara da suna FFK ya jinjinawa kungiyar PANDEF ta ‘yan Neja-Delta.
PANDEF ta yi daidai wajen ajiye Ahmad Gumi a matsayinsa, a cewar tsohon Ministan.
Ahmad Gumi ya tsayawa Falasdinawa
Yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin Isra'ila da Hamas, ana kashe mutanen Falasdinu, ana da labari Sheikh Ahmed Gumi ya dauki mataki.
Dr. Gumi ya bude asusun bada tallafi ya kuma shawarci al'ummar Musulmai da su hada kai wajen taimakawa 'yanuwansu a addini da ke ketaren.
Asali: Legit.ng