Jami’an NDLEA Sun Kame Tan 6 Na Ganyen Maye a Jihohin Najeriya Shida 5, Bayanai Sun Fito

Jami’an NDLEA Sun Kame Tan 6 Na Ganyen Maye a Jihohin Najeriya Shida 5, Bayanai Sun Fito

  • Jami'an hukumar NLDEA sun yi nasarar kame wasu haramtattun kayayyakin bugarwa a jihohin Najeriya 5
  • An kwato kayayyakin ne da suka hada da tabar wiwi da tramadol a yayin da ake ci gaba da yaki shan miyagun kwayoyi
  • Dalla-dalla kakakin NDLEA ya bayyana irin kayayyakin da aka kwato da kuma yadda aka kwato su

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

FCT, Abuja - Hukumar NDLEA ta kama sama da tan shida na ganyen maye a jihohin Ondo, Oyo, Legas, Edo da kuma Gombe, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana haka a Abuja ranar Lahadi, inda ya ce an kama kaya mai nauyin kilogiram 2,197 a wasu yankuna guda hudu a wasu sassan jihar Ondo cikin kwanaki hudu.

Kara karanta wannan

Ya kamata CBN ta sa a daina amfani sabbin takardun Naira da Buhari ya kawo, malami ya fadi dalilai

An kama kayan maye a jihohi 5
Yadda aka kama kayan maye a wasu jihohin Najeriya | Hoto: NDLEA
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa an kama 1,165.5kg a Uso, karamar hukumar Owo ta jihar Ondo a ranar Laraba, yayin da aka kama 691kg na ganyen a dajin Ukugu da ke Ipele, a jihar ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanin kakakin NDLEA

A cewar kakakin:

“An kama wani wanda ake zargi mai suna Ifeanyi Abuguja, mai shekaru 32 da kilogiram 87 a ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba a hanyar Agula, Ogbese, a karamar hukumar Akure ta Arewa.
“A Kasuwar Ogbese dake karamar hukumar jihar Ondo, an kama kilogiram 253.5 na kayan a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba.”

Babafemi ya kara da cewa, an kama wasu mutane biyu, Ayo Dele, mai shekara 19, da Olaitan Ahmed, mai shekaru 23, tare da giram 160 na tabar wiwi a unguwar Inalende da ke Ibadan a ranar Lahadi, 22 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Tunji Olaopa: Muhimman Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban FCSC

Aikin bin kwakwaf da jami'an suka yi ya kai ga bankado wurin ajiyar miyagun magunguna a yankin, inda aka kwato kilogiram 332 na na tabar wiwi, rahoton Peoples Gazette.

Sauran kayan da aka kwato

Kakakin ya kuma bayyana cewa, jami’an NDLEA na rundunar ‘yan sandan Legas sun kwato wata mota makare da mugun kaya mai nauyin kilogiram 209 a unguwar Okun Ajah da ke jihar a ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba.

Babafemi ya kara da cewa jami’an NDLEA a jihar Gombe sun kwato tuli 401 na tabar wiwi da aka jefar da gangan a ranar Asabar.

Ya kuma ce, baya ga kayan mai nauyin kilogiram 392, an kuma kwato kwayoyin tramadol 21,000 a unguwar Tumfure da ke jihar ta Gombe.

An kama mata da kayan maye

A wani labarin na daban, hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta damke wata mata dauke da kunshin hodar iblis 52 a filin sauka da tashin jiragen sama na Aminu Kano a jihar Kano.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa NDLEA ta kama matar mai suna, Bilkisu Mohammed Bello, yayin da take yunkurin kama jirgi zuwa kasar Saudiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.