Kotun Koli: Babban Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abin da Zai Faru Bayan Yanke Hukunci

Kotun Koli: Babban Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abin da Zai Faru Bayan Yanke Hukunci

  • Peter Obi na jam'iyyar Labour Party (LP) ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasan Najeriya, kuma a halin yanzu shi da magoya bayansa sun shiga tsilla-tsilla
  • Wani ɗan takarar da ya sha kaye a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ɗan takarar jam'iyyar PDP, zai yi jawabi mai muhimmanci ga manema labarai a ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba
  • Hakan na zuwa ne bayan kotun ƙoli ta yi watsi da dukkanin ƙararrakin da ƴan adawa suka shigar kan nasarar da Shugaba Bola Tinubu

FCT, Abuja - Yayin da ƴan Najeriya ke cigaba da mayar da martani kan hukuncin da kotun koli ta yanke, shugaban cocin Glorious Mount of Possibility, David Elijah Kingleo, ya ce wasu ƴan Najeriya da ba su ji daɗi ba za su gudanar da zanga-zanga siyasa.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Halarci Taro Na Musamman Bayan Hukuncin Kotun Koli, Ya Sanya Hotuna

Da yake magana kwanan nan a gidan talabijin na Possibility Tv, fasto Elijah ya ce ƴan Najeriya da dama za su taru a fitattun wurare a ƙasashen ƙetare domin nuna rashin jin daɗinsu da hukuncin da kotun koli ta yanke wanda ya tabbatar da zaɓen shugaban kasa Bola Tinubu.

Fasto Elijah ya yi magana kan hukuncin kotun koli
Fasto Kingleo David Elijah ya ce za a yi zanga-zanga bayan hukuncin kotun koli Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar, Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

Hukuncin kotun ƙoli: fasto ya hango zanga-zangar da aka ɗauki nauyi

Kotun ƙoli ta yi watsi da ƙararrakin ƴan adawa tare da tabbatar da nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na watan Fabrairun 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasto Elijah ya bayyana cewa:

"Na shiga cikin ruhaniyya sannan na ga ana ta caccakar kotun ƙoli. A duk inda kuke, ina ba ku maganar ubangiji."

"Ina ganin mutane su na tafiya a ƙasashen waje, mutane suna fitowa a kan tituna ɗauke da alluna daban- daban, mutane sun fara cewa ba za mu amince da hakan ba. Wasu mutane za su fara ɗaukar nauyin ƴan Najeriya waɗanda ba su ji daɗin hukuncin da kotun ƙoli ta yanke ba."

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Bayyana a Karon Farko Bayan Ya Sha Kashi Hannun Tinubu a Kotun Ƙoli

Ayodele Ya Gargadi Atiku, Obi Kan Zuwa Kotun Koli

A wani labarin kuma, fasto Elijah Babatunde Ayodele, ya buƙaci Atiku Abubakar da Peter Obi da kada su ɗaukaka ƙara zuwan kotun ƙoli.

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Fasto Elijah Ayodele, ya bayyana cewa matakin Peter Obi da Atiku na zuwa kotun ƙoli asarar dukiya ce kawai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel