Miyagun Yan Bindiga Sun Kai Hari a Katsina, Sun Halaka Mutum 3 da Yin Awon Gaba da Wasu da Dama
- Ƴan bindiga sun kai mummunan farmaki a ƙauyen Domawa da ke jihar Katsina inda suka halaka mutum uku
- Miyagun ƴan bindigan a yayin harin sun kuma yi awon gaba da wasu mutane masu yawa waɗanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
- A ƙauyen Sukola na ƙaramar hukumar Bakori wasu ƴan bindiga sun sace ƴan mata biyar da suka je bikin ɗaurin aure
Jihar Katsina - Aƙalla mutum huɗu ciki har da dan sanda guda ɗaya ne aka kashe yayin da aka yi awon gaba da wasu da dama a lokacin da ƴan ta'adda suka kai hari a Domawa a ƙaramar hukumar Danmusa ta Jihar Katsina a daren ranar Alhamis.
An kuma sace wasu ƴan mata biyar da wani mutum ɗaya a wani hari na daban da aka kai Sukola, da ke ƙaramar hukumar Bakori a jihar.
Yadda harin ya auku
Jaridar Premium Times ta ambato wata majiya na cewa ƴan ta'addan sun kai hari a cikin ƙauyen na Domawa ne ƴan mintuna kaɗan bayan ƙarfe 9:00 na dare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ya bayyana cewa:
"Ƴan ta'addan sun shiga cikin ƙauyen inda suka fara harbi ba kakkautawa domin tsoratar da mutane. Mutum ukun da ƴan ta'addan suka kashe, ƴan ta'addan sun ɗauke su a matsayin barazana, domin a lokacin da (ƴan ta’addan) suka ce su bi su, sai suka ƙi."
Ya bayyana sunayen waɗanda aka kashe a matsayin Sa’idu Mai Kyaran, Na Doguwa da Suyudi Mai Tabarma yayin ya ce sunan ɗan sandan Hassan.
An sace baƙin ɗaurin aure biyar
A yankin kudancin jihar Katsina, ƴan ta'addan sun kai wani hari da ya kai ga yin garkuwa da wasu ƴan mata biyar da suke halartar wani bikin ɗaurin aure a ƙauyen Sukola.
An kuma yi garkuwa da wani mutum ɗaya mazaunin ƙauyen.
Wani shugaban matasa a ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa:
"Su (ƴan matan) sun fito ne daga ƙauyuka daban-daban da ke kewayen Sukola. Sun je kauye ne domin taya murna ga wata ƙawarsu da za a yi bikinta a ranar Asabar. Kun san mata suna da shagulgulan da suke kafin ɗaurin aure, bayan an tashi shagalin dare ne ƴan ta'adda suka far wa ƙauyen."
Ya bayyana sunayen ƴan matan da aka sace matsayin Maryam Sani, Maijidda Kabir, Abida Matthew da Maryam Ibrahim. Ya ce bai san sunan ta ƙarshen su ba.
A yayin harin da aka kai da misalin ƙarfe 11:00 na dare, majiyar ya ce ƴan ta'addan sun zo ne da “makamai da dama,” inda suka toshe duk wata hanyar shiga cikin ƙauyen tare da cigaba da harbe-harbe domin haifar da ruɗani.
Legit Hausa ta tuntubi muƙaddashin kakakin rundunar ƴan sanda jihar Katsina, Abubakar Sadiq, domin samun ƙarin bayani kan ƙoƙarin da ake wajen ceto ƴan matan, bai dawo da saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Gwamna Radda Ya Sha Alwashin Kin Tattaunawa da Yan Bindiga
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya sake nanata ƙudirinsa na ƙin hawa kan teburin sulhu da ƴan bindiga.
Gwamnan ya bayyana cewa ko matarsa aka kama cikin ƴan bindiga, sai ya ɗamkata a hannun hukuma.
Asali: Legit.ng