“A Dunga Hankali da Yan Aiki”: Wasu Iyali Sun Kadu Bayan Kama Mai Aikinsu a Wajen da Bai Kamata Ba

“A Dunga Hankali da Yan Aiki”: Wasu Iyali Sun Kadu Bayan Kama Mai Aikinsu a Wajen da Bai Kamata Ba

  • Wasu iyali a Najeriya sun cika da mamaki bayan sun kama mai yi masu aikin share-share tana haurawa cikin gidan ta taga
  • A bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya, iyalin sun ce an dauki yarinyar aiki ne domin share masu harabar gidan
  • Matar ta kadu lokacin da masu gidan suka kamata tana kokarin haura taga

Wasu iyali sun kama mai yi masu aikin share-share tana kokarin shiga cikin gidansu ta taga.

Iyalin sun ce sun lura cewa yarinyar tana haurawa cikin gidan ta taga a duk lokacin da masu gidan basa nan.

An kama mai aiki a windo
“A Dunga Hankali da Yan Aiki”: Wasu Iyali Sun Kadu Bayan Kama Mai Aikinsu a Wajen da Bai Kamata Ba Hoto: TikTok/@king_cjohn.
Asali: TikTok

An tattaro cewa an dauko hayar yarinyar ne domin ta dunga share harabar gidan kawai, amma sai aka kama ta tana shiga cikin ainahin gidan ta taga.

An kama mai aikin share-share tana kokarin haura taga

Kara karanta wannan

“Ke Attajira Ce”: Jama’a Sun Yi Martani Yayin da Budurwa Ta Fasa Asusunta, Ta Baje Kolin Kudin

An gano matashiyar yarinyar a kan taga tana kokarin shiga ciki, lokacin da iyalin suka shigo suka kama ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kadu matuka bayan an kama ta. Shafin @king_cjohn ne ya yada bidiyon a TikTok.

An rubuta jikin bidiyon:

"Don Allah ku dunga hankali da wadannan yan matan masu aiki. Kalli inda take bi take shiga ciki idan ba ma nan."

@king_cjohn ya kuma bayyana a sashin sharhi:

"Ba mu rufe ta a cikin harabar gidan ba. Ainahin babban kofar shiga a bude take, kuma an rufe gaba daya dakunan don haka ta shiga ta taga don yin sata."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kai bidiyon mai aiki

@Ebere ta ce:

"Ga ku da ba ku fahimta ba, an dai dauketa aikin share harabar gidan ne sannan sai ta tafi. Idan ta zo ta ga masu gidan basa nan, sai ta bi ta taga ta shiga cikin ainahin gidan don yin sata ku daina caccakar wanda ya nadi bidiyon idan ba ku fahimci abun da ya faru ba."

Kara karanta wannan

“Dadina Da Gobe Saurin Zuwa”: Kalaman Mawaki Rarara Sun Tayar da Kura a Tsakanin Yan Najeriya

@Jas__min ta yi martani:

"Kuna rufe ta a ciki ne? Don ban fahimci dalilin da zai sa ta dunga bi ta taga ba."

@Efe_money123 ya ce:

"Me yasa babu abun kariyar taga?"

Matashi ya koka kan hana shi hakkin aure

A wani labarin kuma, wani mutum ya ce a yanzu yana tarawa da wata mata a wajen gidansa na sunnah a duk lokacin da matarsa ta hana shi hakkinsa na auratayya.

A wani labari da ya yadu a Twitter, mutumin ya ce matarsa na yawan korafi, tana mai ba shi dalilai da suka sa ba za su iya raya sunnah ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng