Wani Mutum Ya Yi Ikirarin Soya Kaza Da Ruwa, Ya Saki Bidiyon Tsarin Da Ya bi

Wani Mutum Ya Yi Ikirarin Soya Kaza Da Ruwa, Ya Saki Bidiyon Tsarin Da Ya bi

  • Wani mutum ya ce ya yi amfani da ruwa wajen soya kaza, kuma ya nuna tsarin da ya bi a cikin wani bidiyo da ya yadu
  • Mutumin ya dage cewa babu ko digon mai a cikin tukunyar suyan kuma cewa kazar ta soyu yadda yake so
  • A halin da ake ciki, masu amfani da TikTok sun dage cewa ba za a taba iya suyar kaza da ruwa ba, sannan wasu sun ce tafasa ta ya yi

Wani mutum ya bayyana cewa ana iya soya kaza da ruwa kadai ba tare da an yi amfani da mai ba, kamar yadda mutane da dama ke yi.

Mutumin ya wallafa wani bidiyo a TikTok sannan ya nuna tsarin da ya bi wajen samun soyyayiyar kaza.

Wani mutum ya ce ya soya kaza da ruwa maimakon mai
“Tafasa Ta Kayi”: Wani Mutum Ya Yi Ikirarin Soya Kaza Da Ruwa, Ya Saki Bidiyon Tsarin Da Ya bi Hoto: TikTok/@fyruta.
Asali: TikTok

A cikin bidiyon, mutumin ya daura tukunyar suya kan wuta, ya zuba ruwa sannan ya bari ya tafasa.

Kara karanta wannan

“Ina Samu a Wajen Wata Matar”: Magidanci Ya Koka Yayin da Matarsa Ke Hana Shi Hakkinsa Na Aure

Yayin da ruwan ya fara tafasa, sai mutumin ya zuba yankan naman kazarsa a cikin ruwan sannan ya bari ya ci gaba da tafasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da kazar ta tafasa, sai ya zuba sinadaran dandano iri-iri a ciki. Ya bari ruwan ya kafe sannan ya rufe tukunyar suyar.

Lokacin da ya fito da kazar, ta yi rakau-rakau. Ya ce tun da ya koyi yadda ake soya kaza da ruwa, ya daina amfani da mai. Sai dai kuma, wasu mabiyansa sun nuna shakku a kansa, sannan wasu sun bayyana cewa tafasa kazar ya yi. @fyruta ne ya wallafa bidiyon.

Kalli bidiyon a kasa:

Yan TikTok sun yi martani

@Adriaan_M ta ce:

"Kowa na da hikima sosai."

@lyssa webb ta ce:

"Na taya ka murna! Mu tsoffin hannu muna kiran sa da tafasasshiyar kaza."

@mirrorimagevaletsuk ta ce:

Kara karanta wannan

Ana Min Kallon Ba Zan Iya Ba Saboda Na Iya Rawa, Gwamnan PDP

"Ka dai hada kazar sinadarin kori."

@Kyo758 ta yi martani:

"A halin da ake ciki, baaba, ana kiran wannan da kazar miya."

@Ja’MericanBoy ya ce:

"Wow, ka dafa wata tafasasshiyar gaza."

Matashiya ta saki bidiyon yadda ake man ja

A wani labarin, jama'a sun yi cece-kice kan bidiyon wata matashiya da ke nuna muhallin da take sarrafa man ja.

Bidiyon da aka wallafa a Twitter ya bai mutane mamaki saboda wurin na da datti sosai da tabo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng