“Ke Attajira Ce”: Jama’a Sun Yi Martani Yayin da Budurwa Ta Fasa Asusunta, Ta Baje Kolin Kudin

“Ke Attajira Ce”: Jama’a Sun Yi Martani Yayin da Budurwa Ta Fasa Asusunta, Ta Baje Kolin Kudin

  • Wata matashiya yar Najeriya ta garzaya dandalin soshiyal midiya domin baje kolin kudaden da ta tara a asusun ajiyarta
  • Ta fito da asusunta sannan ta fasa shi bayan kammala karatunta domin nunawa duniya tarin kudin da ta mallaka
  • Yayin da abun ya burge mutane da dama, wasu sun yi kokarin cinkar nawa ta tara domin lashe gasar N10k

Wata matashiya yar Najeriya ta nunawa duniya makudan kudaden da ta tara bayan ta fasa asusun ajiyarta na katako.

Da take wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda ta fasa asusun nata, ta rubuta, "Ku cinka nawa ne kudin idan aka hada sannan N10k ya zama naka."

Budurwa ta fasa asusun ajiyarta
“Ke Attajira Ce”: Jama’a Sun Yi Martani Yayin da Budurwa Ta Fasa Asusunta, Ta Baje Kolin Kudin Hoto: @lohreyy
Asali: TikTok

Kamar yadda matashiyar, @lohreyy ta bayyana, ta fara ajiye kudin ne a ajinta na karshe a makaranta sannan ta fasa shi bayan ta kammala makarantar.

Kara karanta wannan

“Ku Zo Da Barkono”: Yar Najeriya Ta Lissafo Muhimman Abubuwan Da Mutum Zai Riko Idan Zai Koma Kanada

Ta fito da kudade masu yawan gaske manya da kanana sannan ta mimmikar da su tsaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan nan, sai ta rike su ta haskawa kamara yayin da take tunanwa duniya su cike da murna. Mutane da dama sun yi kokarin fadin nawa ne kudin da ta tara a asusun nata a kokarinsu na lashe gasar N10k din da ta saka."

Kalli bidiyon a kasa:

Mutane sun yi martani kan kudin da ta tara

alexanderifechigh4 ta ce:

"Don Allah za ki iya koya mun yadda ake tara kudi."

EMELA ta ce:

"Baaba zan tara kudi yau da gobe kudin zai taimaka mun."

raphaelhappiness3 ta ce:

"Mutumin da ke raye ne yake tara kudi, na yi amfani da 3500 dina na siya lemun chivita mai sanyi da biskiti."

Princess_Ngo ta ce:

"Miliyan 1 tunda babu wanda ya fadi amsar daidai."

Kara karanta wannan

Bashin $3.5bn: Tinubu Ya Fadi Yadda Zai Kasafta Kudaden Don Amfanar Talakawa, Ya Fadi Tsawon Lokacin Biya

Ameerah ta ce:

"Baaba ke miloniya ce."

DARA's Stitches ta ce:

"Duk ku yi ta wasa ba za ku taba cinka ba..koda kun cinka za ta ce maku ba haka ba."

Thiana255 ta ce:

"Da tsintsiya nake cike nawa a hankali duk san da na tashi ba kudi...har yanzu asusun na nan sabo da shi, duk kudaden ciki sun kare."

Matashiya ta tara kudi a asusu

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa wata baiwar Allah ta cika da farin ciki yayin da ta fasa dan akwatin da ta yi asusun kudade bayan ta kwashe watanni tana ajiya.

Wani faifan bidiyo mai daukar hankali da aka yada a TikTok, ya dauki lokacin da ta fasa asusun don bayyana makudan kudin da ta tara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng