Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Hudu Yayin da Suka Kai Farmaki a Jihar Zamfara
- 'Yan bindiga sun kai mummunan hari garin Maru, hedkwatar ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara
- Rahoto ya nuna cewa maharan sun shiga fadar mai martaba Sarkin Maru amma Allah ya sa ya tsallake sharrinsu
- Gwamnatin Zamfara ta sanar da kulle kasuwar garin da ke ci duk ranar Jumu'a saboda abin da ka iya zuwa ya dawo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Zamfara - Mutum huɗu sun rasa rayukansu biyo bayan wani hari da yan bindiga suka kai garin Maru, hedkwatar ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Wani haifaffen garin, Mohammed Bawa, ya shaida wa jaridar Punch cewa maharan sun kuma shiga fadar mai martaba Sarkin Maru yayin harin.
Sai dai duk da Sarkin Maru, Abubakar Maigari, ya samu nasarar tsira daga sharrin 'yan ta'addan amma sai da suka kashe dogari ɗaya kuma suka jikkata wasu.
A cewar Bawa, Motar Sarkin ta yi kaca-kaca sakamakon wutar da yan bindigan suka buɗe a fadar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ƙara da bayanin cewa 'yan bindigan sun sake komawa garin ranar Alhamis suna neman Sarkin amma ba su ganshi ba, daga nan suka shiga gida-gida, suka kashe mutum huɗu.
A rahoton Channels tv, Mutumin ya ce:
"Yan bindigan sun shiga fadar Sarkin inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi a kokarinsu na kashe shi, amma Allah ya tseratar da shi. Sun kashe dogari ɗaya kana suka lalata motocin wurin."
"Bayan sun sake dawowa jiya da daddare, ba su ga Sarkin ba a fada, suka bi gida-gida suna nemansa, yayin haka ne suka kashe mutane huɗu. Yau Jumu'a aka musu jana'iza kamar yadda Musulunci ya tanada."
Gwamnati ta garƙame kasuwar Maru
A halin da ake ciki, Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da kulle babbar kasuwar Maru saboda fargabar 'yan bindiga ka iya kai hari yau Jumu'a, ranar da kasuwar ke ci.
A wata sanarwa, kwamishinan yaɗa labarai na Zamfara, Munnir Haidara ya ce:
"Sakamakon yanayin tsaro a garin Maru, Gwamnatin jiha ta kulle kasuwar garin har sai yanayin tsaro ya daidaita."
"Mai girma gwamna Dauda Lawal na miƙa ta'aziyya ga iyalan waɗan da suka rasa rayukansu a harin 'yan bindiga na daren ranar Alhamis."
Wani mazaunin Maru, Abubakar Usman, ya shaida wa Legit Hausa cewa tabbas yan bindiga sun ci karensu babu babbaka yayin harin.
Ya ce tun ƙarfe 1:00 na tsakar dare suka kai harin, suka buɗe wuta har wajen karfe 5:30 na asuba kuma jami'an soji sun taɓuka abin a zo a gani gaskiya.
"Tabbas wannan labari gaskiya ne, wallahi muna cikin mawuyacin hali a Maru, sojoji sun yi ƙoƙari da ba a san yawan mutanen da zasu kashe ba a harin."
"Sun farmaki fadar Sarki amma Allah bai ba su nasara ba, amma sun haɗu da mahaifin abokina suka kashe shi nan take, muna buƙatar Addu'a."
Ƴan daba sun miƙa wuya a Kano
A wani rahoton kuma Ɗan daba da rundunar 'yan sanda ke nema ruwa a jallo a jihar Kano ya miƙa wuya tare da wasu 'yan baranda 40 ranar Alhamis.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa,.ya ce duk sun tuba daga aikata laifukan daba kuma sun miƙa makamansu.
Asali: Legit.ng