Wani Hatsabibin Dan Daba da Ake Nema Ruwa a Jallo Ya Mika Wuya Ga Yan Sanda a Kano

Wani Hatsabibin Dan Daba da Ake Nema Ruwa a Jallo Ya Mika Wuya Ga Yan Sanda a Kano

  • Ɗan daba da rundunar 'yan sanda ke nema ruwa a jallo a jihar Kano ya miƙa wuya tare da wasu 'yan baranda 40 ranar Alhamis
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce duk sun tuba daga aikata laifukan daba kuma sun miƙa makamansu
  • Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Gumel ya bada umarnin ɗaukar bayanansu da kuma canza musu tunani

Jihar Kano - Wani hatsabibin ɗan daba da rundunar 'yan sanda reshen jihar Kano ta ayyana nemansa ruwa a jallo tun a watan Agusta, 2022, ya miƙa kansa ga jami'an tsaro.

Ɗan daban ya miƙa wuya ga dakarun 'yan sanda tare da ƙarin wasu 'yan daba 40 a jihar Kano, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Karin 'yan daba 41 sun aje makamai a Kano.
Wani Hatsabibin Dan Daba da Ake Nema Ruwa a Jallo Ya Mika Wuya Ga Yan Sanda a Kano Hoto: PoliceNG
Asali: UGC

Idan baku manta ba rundunar 'yan sanda ta ayyana Abba Barakita mazaunin Unguwar Ɗorayi, Nasir Abdullahi wanda aka fi sani da Chile Maidoki da ke Layin Falwaya Kurna Makabarta a matsayin waɗan da take nema ruwa a jallo.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sama da 100 Sun Sheƙa Lahira Yayin da Jirgin Sojin Sama Ya Sakar Musu Wuta a Jihohi 2

Haka kuma ta bayyana neman Hantar Daba wanda ke zaune a Unguwar Kwanar Ɗawisu ruwa a jallo amma tun da jima wa Nasir Abdullahi ya miƙa kansa ga 'yan sanda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ɗan daban ya miƙa wuya

A halin yanzu, ɗaya daga cikin waɗan nan 'yan daba uku da ake nema ruwa a jallo, Abba Barakita ya miƙa wuya ga jami'an 'yan sanda ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba.

Haka nan kuma ya sanar da cewa ya tuba ya daina harkokin dabanci wanda tun farko ake zarginsa da aikata wa.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce tubabben ɗan daban ba miƙa wuya kaɗai ya yi ba, ya jawo wasu 40 sun miƙa wuya.

Ya kuma kara da cewa dukkan 'yan daban da suka tuba sun miƙa makamansu ga jami'an tsaro, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan Biyan Makudan Kudin Fansa, An Sako Babbar Malamar Jami'ar da Yan Bindiga Suka Sace

A cewarsa, sakamakon haka ne kwamishinan yan sandan Kano, CP Muhammed Usaini Gumel ya bada umarnin ɗaukar bayanan tubabbun 'yan daban.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda 100

A wani labarin na daban Sojin saman Najeriya sun halaka 'yan bindiga sama da 100 a waninruwan bama-bamai da suka yi a iyakar jihohin arewa biyu.

Hedkwatar tsaro ta ƙasa DHQ ta bayyana cewa a cikin mako ɗaya, sojoji sun aika gomman da yan bindiga lahira, sun damƙe wasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262