Tashin Hankali Yayin da Hatsabiban Yan Fashi Suka Gudu Daga Gidan Yari a Katsina
- Mazauna cikin garin Katsina sun shiga tashin hankali bayan wasu hatsabiban 'yan fashi sun tsere daga gidan gyaran hali
- Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta tabbatar da faruwar lamarin ga yan jarida, inda ta ce har ta sake kama ɗaya daga ciki
- Ta ce wannan ba sabon abu bane amma tana kan aikin zakulo duk inda ɗayan fursunan ya shiga, a sake kamo shi
Jihar Katsina - Labarin tserewar wasu hatsabiban ƴan fashi da makami daga gidan gyaran halin da ake tsare da su ya jefa tsoro da tashin hanhali tsakanin mutanen cikin garin Katsina.
Rahoton jaridar Premium Times ya nuna cewa har yanzun babu cikakken jawabi kan ranar da ƴan fashin guda 2 suka gudu domin jami'an tsaro sun ƙi cewa komai kan hakan.
Amma wani babban jami'in hukumar 'yan sanda da ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da hurumin magana da ƴan jarida, ya ce an sanar da 'yan sanda batun ɓatan fursunonin.
Ya tabbatar da cewa an sanar da hukumar ƴan sanda batun tserewar Fursunonin ranar 16 ga watan Oktoba, 2023, amma ya ƙi ƙara bayani kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayani kan ƴan fashin da suka gudu
Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da aikata laifin fashi, Ibrahim Lawal, wanda ake kira da Abba Kala, ba ƙaramin hatsabibin ɓarawon motoci bane.
Aƙalla sau biyu jami'an tsaro suka damƙe shi bisa zargin aikata manyan laifuka ciki harda fashi da makami. Sai dai ba a bayyana sunan ɗayan Fursunan ba.
Hukumar gyaran hali ta magantu
Kwanturolan hukumar kula da gidajen gyaran hali reshen jihar Katsina, Muhammad Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wasu 'yan jarida ranar Litinin.
Ya ce ya zuwa yanzu sun sake cafke ɗaya daga cikin waɗanda suka gudu, inda ya ƙara da cewa ba hukumar gidajen gyaran hali kaɗai ke fama da guduwar waɗan da ake zargi ba.
Haruna ya ce hukumar ta fara gudanar da bincike domin gano yadda fursunonin suka yi nasarar tserewa daga gidan yarin.
Ya ce:
"Kamar yadda kuka sani, guduwar waɗanda ake zargi daga hannun jami'an tsaro ba sabon abu bane, ba zancen ɓoye-boye, mutum 2 da ke jiran shari'a sun tsere daga Kurkuku."
"Cikin sa'a da kokarin jami'ai da sauran hukumomin tsaro da haɗin kan jagororin tashoshin mota a jihar nan, mun sake kamo ɗaya daga ciki, ɗayan ma zamu kama shi ba da daɗewa ba."
Yan bindiga sun kashe ƴan gudun hijira
A wani rahoton kuma Tsagerun 'yan bindiga sun tare 'yan gudun hijira, sun harbe su har lahira a jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya.
Rahotanni sun bayyana cewa mutanen uku da aka kashe sun tafi kamun kifi, ba zato 'yan ta'addan suka tare su kuma suka kashe su.
Asali: Legit.ng