Jerin Sunaye: Najeriya, Masar da Sauran Kasashen da Amurta Ba Ta da Ambasada da Dalilai
- Amurka ta koka kan rashin jakadu a kasashen duniya akalla 31 ciki har da Najeriya da kuma Masar watau Egypt
- Mathew Miller, mai magana da yawun gwamnatin Amurka, shi ne ya bayyana haka, inda ya ce har yau majalisa ba ta amince da naɗin Jakadun ba
- Wannan bayani na Miller na zuwa ne yayin da Amurka ke tallafa wa Isra'ila, wadda ke ci gaba da ruwan bama-bamai kan Gaza tun bayan harin Hamas
White House, US - Amurka ta bayyana cewa har kawo yanzu ba ta da jakada a Najeriya duk da yadda dangantaka ke ƙara kyau tsakanin ƙasashen biyu.
A wani jawabi da kakakin gidan gwamnatin Amurka, Mathew Miller, ya wallafa a manhajar X, ya yi ƙarin haske kan ƙasashen da US ba ta da wakilai.
A cewar Miller, har yanzu Amurka ba ta da jakada a Najeriya da wasu ƙasashe 31 saboda majalisar dattawan ƙasar ba ta kai ga amince wa da waɗanda aka naɗa ba.
Sunayen ƙasashe 31 da babu jakadan Amurka
Baya ga Najeriya, mun tattaro muku sauran ƙasashen da Amurka ba ta da wakilci a faɗin duniya, ga su kamar haka:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Lebanon
2. Isra'ila
3. Masar
4. Azerbaijan
5. Lithuania
6. Haiti
7. Tarayyar Afirka
8. Turkmenistan
9. Albania
10. Zimbabwe
11. Barbados
12. Peru
13. Ecuador
14. Cabo Verde
15. Laos
16. Nijar
17. Djibouti
18. Malaysia
19. Gabon
20. Burundi
21. Croatia
22. Guatemala
23. Liberia
24. Somalia
25. Bahamas
26. Colombia
27. Cambodia
28. Montenegro
29. Timor-Leste
30. Marshall Islands
31. Burkina Faso
Dangantakar Amurka da Isra'ila
Wannan na zuwa ne yayin da ƙasar Amurka ta nuna goyon bayanta ga Isra'ila kan ruwan bama-baman da take yi a gaza tun bayan harin da ƙungiyar Hamas ta kai kan 'yan ƙasar Isra'ila.
Joshua Iginla, shugaba kuma wanda ya kafa majami'ar Champions Royal Assembly ya roƙi shugabannin duniya su tabbata wannan yaƙin na Isra'ila da Gaza bai rikiɗe ya zama yaƙin duniya na III ba.
A wani bidiyo da ya wallafa a Youtube, Malamin addinin ya bayyana cewa ya hango babban yaƙi na tafe.
Antonio Guterres Ya Soki Isra'ila
A wani rahoton kuma Yayin da ake ci gaba da gwabza yaki tsakanin Isra'ila da Hamas, Majalisar Dinkin Duniya ta yi martani.
Sakataren Majalisar, Antonio Guterres ya zargi Isra'ila da saba dokokin kasa da kasa na jin kai a harin da su ke kai wa.
Asali: Legit.ng