Lambar Buhari, Jonathan Sun Fito, Za a Binciki N11tr da Gwamnati ta Kashe Kan Matatu

Lambar Buhari, Jonathan Sun Fito, Za a Binciki N11tr da Gwamnati ta Kashe Kan Matatu

  • Sanata Barau Jibirin ya zauna a kujerar Godswill Akpabio, ya jagoranci zaman farko da majalisar dattawa ta yi a makon nan
  • A zaman ne Sanata Sunday Karimi ya kawo maganar makudan kudin da aka kashe domin a gyara matatun man Najeriya
  • Duk da tulin kudin da aka kashe na sama da Naira tiriliyan 11, Sanatocin sun ce har gobe matatun su na nan dai yadda su ke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - A ranar Talata, Barau Jibirin ya jagoranci zaman da aka yi a majalisar dattawa, inda aka tabo batun kwangilar gyaran matatun mai.

VON a rahoton da ta fitar, ta bayyana cewa Sunday Karimi (Kogi APC) ya kawo kudirin yin binciken kudin da aka kashe kan gyaran matatun.

Sanata Sunday Karimi ya bijiro da maganar ne domin rage facaka da dukiyar gwamnati, ganin makudan kudin da aka batar da sunan gyara.

Kara karanta wannan

Bashin $3.5bn: Tinubu Ya Fadi Yadda Zai Kasafta Kudaden Don Amfanar Talakawa, Ya Fadi Tsawon Lokacin Biya

Shugaban kasa da shugaban majalisa
Majalisa ta binciki gwamnatin tarayya Hoto: @SPNigeria
Asali: Twitter

Majalisa ta kafa kwamitin bincike

A cewarsa, daga 2010 zuwa shekarar nan, abin da aka kashe a kan matatun danyen mai hudu sun kai N11.35tr, amma ba a ga tasirin hakan ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jibirin ya umarci Sanata Isah Jibrin ya zama shugaban kwamitin musamman da zai duba yadda aka batar da kudi saboda a iya tace mai a gida.

‘Yan kwamitocin harkokin gas, mai, kasafin kudi da na asusun gwamnati su na cikin wannan kwamiti da zai gabatar da bincike na musamman.

Jaridar Business Day ta ce ragowar ‘yan kwamitin su ne: Abdullahi Yahaya (PDP, Kebbi) Adamu Alero (PDP, Kebbi), Ifeanyi Ubah (APC, Anambra).

Kwamitin zai gabatar da bincikensa, ya mika rahoto ga majalisa nan da makonni hudu.

Sanatoci sun goyi bayan binciken

Da aka kawo maganar a zauren majalisa, Aliyu Wadada, Ita Williams da Isah Jibrin sun tofa albarkacin bakinsu kamar yadda P/Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Za a Kawo Karshen Tashin Dala, Ana Sa Ran Shigowar $10bn Nan da ‘Yan Makonni

Sauran wadanda su ka yi magana su ne: Olalere Oyewunmi da Adeola, Olamilekanm.

Ya za a bi domin farfado da Naira?

A rahoton nan, an ji yadda tsohon mataimakin gwamna a babban banki watau Kingsley Moghalu ya ba sababbin Gwamnonin CBN shawarwari.

Farfesan ya fadi abin da zai jawo Dala ta rage mahaukacin tashin da ta ke yi a kasuwa a Najeriya, ya ce a daina dogara da kayan kasashen waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng