“Na Gina Gidaje”: Dan Ibo Da Ke Tuya Kosai a Lagas Tsawon Shekaru 25 Ya Magantu

“Na Gina Gidaje”: Dan Ibo Da Ke Tuya Kosai a Lagas Tsawon Shekaru 25 Ya Magantu

  • Wani dan kabilar Ibo da ke sana'ar kosai a jihar Lagas ya bayyana cewa baya so yaransa su gaji sana'ar da yake yi
  • Mutumin haifaffen dan Ebonyi, wanda ya fara sana'ar tun 1998, ya ce ya yi nasarar gina gidaje da shi
  • Labarin mai kosan ya janyo masa farin jini a wajen masu amfani da soshiyal midiya sannan ya taba zukatan mutane da dama

Chibueze Damian, wani dan kabilar Ibo da ke sana'ar soya kosai ya yadu a soshiyal midiya.

Da aka yi hira da shi, mutumin ya bayyana cewa ya fara siyar da kosai tun 1998 kuma ya shafe fiye da shekaru 20 a kai.

Ya gina gidaje da sana'ar kosai
“Na Gina Gidaje”: Dan Ibo Da Ke Tuya Kosai a Lagas Tsawon Shekaru 25 Ya Magantu Hoto: @foodieinlagos
Asali: TikTok

Chibueze, wanda ake kira da Baba Akara Mushin, ya bayyana cewa ya gina gidaje da sana'ar sannan da shi yake daukar dawainiyar yaransa.

Kara karanta wannan

“Wannan Aure Akwai Matsala”: Rudani Yayin da Bidiyon Wani Ango Da Amarya Ya Jefa Mutane Cikin Damuwa

A cewar haifaffen dan Ebonyi din, ya fara sana'ar da gwangwanin wake daya amma a yau sana'ar ta gabbaka. Chibueze yana kai oda ga kwastamomi a yankin Mushin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce baya so yaransa su gaje shi a sana'arsa. Ya jaddada cewar yana shan wahala ne don rayuwarsu ta yi kyau.

"Ina shan wahala don su ne saboda su yi rayuwa mai kyau."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani ga bidiyon mai kosai

Gideon Kenneth ya ce:

"Na ga wani bahaushe a Obalende wanda ke dafa taliya. ya ce yana wajen tun 1984 ta yaya mutane ke dadewa a sana'a irin haka."

Realsmoney68 ya ce:

"Dan uwana na Ebonyi, Allah ya albarkaci yaranka don su kula da kai, Allah ya albarkaci kasuwancin ka."

rabiatt123 ta ce:

"Matsalarmu a matsayin iyaye, bana so su wahala yadda na wahala, tushen matsalar yara da dama, babu rayuwar duniya da mutum zai fuskanta kamar kalubale."

Kara karanta wannan

Wani Mutum Ya Ajiye Girman Kai, Ya Roki Budurwarsa Ta Hanyar Birgima a Kasa, Bidiyon Ya Bazu

Warrior_Princess ta ce:

"Inyamurai kenan. Abun da kake gani ba mai yiwuwa bane za su sa ya yiwu."

Matashi ya gina gidaje 3 da sana'ar ayaba

A wani labarin, wani hazikin dan Najeriya da ke sana'ar siyar da soyayyen ayaba ya nunawa duniya gidan da yake ginawa.

Mutumin mai suna @adegbengaolusegun ya ce ginin shine gida na uku da ya gina tun bayan da ya fara sana'ar siyar da soyayyen ayaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng