Ma'aikata Sun Sha Alwashin Rufe Majalisun Tarayya da Na Jihohi Ranar Laraba

Ma'aikata Sun Sha Alwashin Rufe Majalisun Tarayya da Na Jihohi Ranar Laraba

  • Ma'aikata sun sha alwashin rufe majalisun tarayya da majalisun dokokin jihohi 36 ranar Laraba mai zuwa
  • Sun yanke wannan hukuncin ne domin fara yajin aiki kan buƙatarsu ta ganin na sakarwa majalisu mara su ci gashin kansu
  • Ƙungiyar ma'aikatan majalisun dokokin ta bayyana cewa wa'adin da ta ɗibarwa gwamnoni ya cika amma ta ƙara mako ɗaya

FCT Abuja - Ma'aikatan kafatanin majalisun dokokin jihohi 36 da kuma na majalisar tarayya sun lashi takobin garkame wuraren ayyukansu a faɗin Najeriya.

Ma'aikatan sun ƙudiri aniyar rufe dukkan majalisun dokokin ƙasar nan har sai an biya musu buƙatarsu ta bai wa ɓangaren masu dokoki damar cin gashin kansu.

Zauren majalisar dokokin tarayya.
Ma'aikata Sun Sha Alwashin Rufe Majalisun Tarayya da Na Jihohi Ranar Laraba Hoto: NASS
Asali: Facebook

Daily Trust ta ce ma’aikatan a karkashin kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya (PASAN) suna nemi gwamnonin jihohi su sakarwa majalisu mara su koma masu cin gashin kansu.

Kara karanta wannan

Hotunan Matasa Maza da Mata Mahaddatan Alkur'ani Sun Cika Gidan Kwankwaso Maƙil Kan Abu 1

Sun buƙaci gwamnonin su gaggauta aiwatar da hakan kamar yadda kudin tsarin mulkin ƙasa 1999 ya tanada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba a lokuta daban-daban sun gudanar da zanga-zangar lumana a kan tituna domin su matsa a biya masu buƙatunsu.

Ma'aikatan sun tabbatar da shirinsu na rufe majalisu a wasu wasiƙu mabanbanta da suka aike wa shugaban ƙungiyar gwamnoni (NGF), shugaban ƙungiyar shugabannin majalisa da DSS.

Meyasa za su shiga yajin aiki?

A cewarsu, sun bai wa gwamnoni wa'adin makonni uku su sakar wa majalisu mara su ci gashin kansu ko kuma su fuskanci yajin aikin ma'aikata.

Dukkan wasiƙun na ɗauke da sa hannun muƙaddashin Sakatare Janar na ƙungiyar ma'aikatan majalisun dokoki PASAN, Agugbue Ugochi Happiness.

Bayan mika wasikun, Happiness ya shaida wa 'yan jarida ranar Litinin cewa kungiyar ta bada wa’adin ne tun ranar 18 ga Satumba, 2023, kuma gwamnonin suka yi watsi da wa’adin har ya kare.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Wasu Ministoci da Jiga-Jigan FG a Villa, Bayanai Sun Fito

Ya ce bayan ƙarewar wa'adin ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, 2023, ƙungiyar ta ƙara wa'adin mako ɗaya domin bai wa jihohin ƙarin damar cika wannan buƙata.

A ruwayar Channels tv, Wani sashin wasiƙar ta ce:

"Saboda haka muna fatan wannan ƙarin zai bada damar cika wannan buƙatu domin daƙile yunƙurin ƙungiyar mu na tsunduma yajin aiki."
"Muna kuma jaddada kudirin mu cewa matukar ba a mana abinda muke so ba zamu umarci mambobi sun shiga yajin aiki."

Fitacciyar Jarumar Fina-Finai Ta Koma APC

A wani rahoton kuma Jarumar Nollywood da ke kudancin Najeriya, Tonto Dikeh, ta sauya sheƙa daga ADC zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Ta samu kyakkyawar tarba daga shugabar matan APC ta ƙasa, Mary Alile, da mataimakin sakataren watsalar a hedkwatar Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262