Hotunan Matasa Maza da Mata Mahaddatan Alkur'ani Sun Cika Gidan Kwankwaso

Hotunan Matasa Maza da Mata Mahaddatan Alkur'ani Sun Cika Gidan Kwankwaso

  • Mahaddatan Alkur'ani mai girma sun cika maƙil a gidan tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso da ke Bampai ranar Litinin
  • Sun je gidan ne domin neman gurbin shiga sabuwar makarantar Islamiyya da Boko, wacce Kwankwaso ya ce zasu horar da Almajirai
  • A cewarsa, makarantar zata koyar da mahaddata Alƙur'ani ilimin Musulunci da na Boko domin rage barace-barace a kan titi

Jihar Kano - Ɗaruruwan matasa maza da mata mahaddatan Alƙur'ani mai girma sun cika maƙil a gidan jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso.

Mahaddatan Littafin Allah mai tsarki sun yi tururuwa a gidan Kwankwaso ne domin neman gurbin shiga makarantarsa ta Islamiyya da kuma Boko.

Hotuna daga gidan Kwankwaso.
Hotuna: Matasa Maza da Mata Mahaddatan Alkur'ani Sun Cika Gidan Kwankwaso Hoto: NNPP Kwankwasiyya
Asali: Facebook

Matasan waɗanda suka ƙunshi maza da mata kuma suna da haddar Alƙur'ani mai girma sun fito ne daga kananan hukumomi 44 na jihar Kano, shafin NNPP Kwankwasiyya ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Masallaci a Lokacin Sallah, Sun Kashe Liman a Jihar Kaduna

Dukkan matasan suna da shekaru tsakanin 15 zuwa 25 kuma an gan su ne a gidan Kwankwaso da ke Bompai suna rubuta sunayensu tare da tantance su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abinda makarantar ta ƙunsa

A 'yan kwanakin nan, Kwankwaso ya bada kyautar ginin da wannan makaranta za ta fara karatu domin kawo ƙarshen barace-baracen Almajirai a kan tituna.

Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar NNPP a zaben 2023 da ya wuce ya ce makarantar wacce aka raɗa wa sunan mahaifinsa, zata ƙoyar da Almajirai ilimin Alƙur'ani da na Boko.

A cewarsa, wadannan Almajirai da za a horar za a basu takardar shedar firamare da sakandare da kuma difloma.

Ya kuma bayyana cewa Almajirai da suka yi rajista za a koyar da su da Ingilishi da Larabci, inda za su yi amfani da satifiket ɗin wajen shiga makarantu, wanda zai taimaka musu wajen neman ilimi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wasu Tsageru Sun Shiga Har Ɗakin Kwana, Sun Kashe Ɗaliba a Jihar Arewa

An tattaro cewa cibiyar ta shirya jadawalin karatu da za a horas da maza da mata cikin kankanin lokaci domin samun takardar shedar firamare da sakandare.

Hotunan yadda mahaddata suka mamaye gidan Kwankwaso

Mun haɗa muku wasu daga cikin Hotunan yadda mahaddatan Alƙur'ani suka mamaye gidan Kwankwaso yau Litinin.

Yadda matasa suka cika maƙil a gidan Kwankwaso.
Hotunan Yadda Matasa Maza da Mata Mahaddatan Alkur'ani Suka Cika Gidan Kwankwaso Hoto: NNPP Kwankwasiyya
Asali: Facebook

Mata mahaddata a gidan Kwankwaso.
Hotuna: Matasa Maza da Mata Mahaddatan Alkur'ani Sun Cika Gidan Kwankwaso Hoto: NNPP Kwankwasiyya
Asali: Facebook

Mahaddata maza a gidan Kwankwaso.
Hotuna: Matasa Maza da Mata Mahaddatan Alkur'ani Sun Cika Gidan Kwankwaso Hoto: NNPP Kwankwasiyya
Asali: Facebook

Yadda ake tantance matasa a gidan Kwankwaso.
Hotuna: Matasa Maza da Mata Mahaddatan Alkur'ani Sun Cika Gidan Kwankwaso Hoto: NNPP Kwankwasiyya
Asali: Facebook

Mahaddata a gidan Kwankwaso.
Hotuna: Matasa Maza da Mata Mahaddatan Alkur'ani Sun Cika Gidan Kwankwaso Hoto: NNPP Kwankwasiyya
Asali: Facebook

An toshe hanyoyin sata a Kano

A wani rahoton na daban Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nanata cewa a lokacin da aka damka masa mulki, bai samu wasu kudi a cikin baitul-malin jihar Kano ba

Abba Gida-Gida ya ce amma a yanzu, gwamnatinsa ta na yi wa talakawanta ayyuka ba tare da kukan karanci ko rashin kudi ba saboda an toshe wasu hanyoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262