An Fara Kutun-Kutun a Kotu Domin Tsige Sabon Shugaban EFCC Daga Rantsar da Shi
- Babban Kotun Tarayya za su raba gardamar da ake yi a kan cancantar Mista Olanipekun Olukoyede na shugabantar hukumar EFCC
- Karar da aka gabatar sun isa Kotun Abuja, kuma Alkali ya nuna zai bada dama domin a iya kalubalantar sabon nadin mukamin da aka yi
- Stanley Okawara da Maxwell Opara su ka yi hayar lauyoyi domin a shigar da karar da za ta iya jawo Olukoyede ya rasa kujerarsa
Abuja – Babban Kotun Tarayya da ke zama a birnin Abuja, ta yi na’am da wasu kararraki da aka shigar domin tsige shugaban hukumar EFCC.
Rahoto ya fito daga Vanguard cewa wasu lauyoyi; Stanley Okawara da Maxwell Opara sun je kotu saboda ayi waje da Olanipekun Olukoyede.
Shari’ar farko mai lamba FHC/KN/CS/280/202 ta na reshen kotun da ke Kano yayin da za a saurari mai lamba FHC/ABJ/CS/1410/2023 a Abuja.
EFCC: Kotu ta karbi karar da aka kai
Alkali Abdullahi Liman a kotun na Kano ya karbi karar, ya tsaida 30 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a soma sauraron karar da aka kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shari’an zai raba gardama game da cancantar Olanipekun Olukoyede ya rike EFCC. Hakan ya na zuwa ne 'yan kwanaki da tantace shi.
Lauyan da ya shigar da karar, Jideobi Johnmar ya na so a dakatar da Mr. Olukoyede, kotu ta fada masa ya fara sanar da wadanda ya ke kara.
EFCC: Ragowar wadanda aka kai kotu
Sauran wadanda ake tuhuma a shari’ar su ne Bola Tinubu, Godswill Akpabio da kuma EFCC.
Ragowar wadanda za su kare kan su a kotun sun hada da: sabon shugaban na EFCC da kuma Muhammad Hammajoda wanda shi ne sakatare.
Business Day ta ce Kotu za ta yanke hukuncin da zai zama makomar Mista Olukoyede.
Za a aika takardar shari’ar zuwa ga shugaban kasa ta ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi, SAN domin bada kariya.
Haka kuma za a sanar da shugaban majalisar dattawa ta hannun akawunsa. Wadanda aka yi kara za su maida martani nan da kwanaki 15.
Shari'ar PDP, LP vs APC
Helen Moronkeji Ogunwumiju wanda ake zargin yaronta ya na APC ta na cikin Alkalan da su ke sauraron shari'ar zaben 2023 gaban kotun koli.
Atiku Abubakar, Peter Obi da Chichi Ojei ba su gamsa da hukuncin da aka yi a baya ba. ‘Yan takaran adawa sun daukaka shari’ar zaben da aka yi.
Asali: Legit.ng