Al'ummar Jihar Zamfara Sun Rubuta Wasika Zuwa ga Tinubu Kan Harin 'Yan Bindiga
- Wasu mazauna garuruwan mazaɓar Sanatan Zamfara ta arewa sun rubuta wasiƙa zuwa ga gwamna da shugaban ƙasa Tinubu
- Mutanen a karkashin kungiyarsu, sun ja hankalin cewa 'yan bindiga na ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankunan su
- A cewarsu, idan har ba a hanzarta kawo karshen lamarin ba to babu wanda ya an waye abin hari na gaba
Jihar Zamfara - Wata ƙungiyar garuruwan jihar Zamfara ta rubuta wasiƙa zuwa ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, kan ƙaruwar hare-haren 'yan bindiga.
Channels tv ta tattaro cewa ƙungiyar ta ja hankalin shugaban ƙasa kan yadda 'yan bindigan jeji ke cin karensu ba babbaka a Ƙauran Namoda da kewaye da ke mazabar Sanatan Zamfara ta arewa.
A buɗaddiyar wasiƙar kungiyar mai suna, 'Zamfara Circle Community Initiatives' (reshen Ƙauran Namoda) mazauna ƙauyukan yankin sun roƙi gwamnati ta kawo musu ɗauki.
Sun roƙi shugaba Tinubu da gwamna Dauda Lawal na Zamfara, "Ku yi duk mai yiwuwa wajen kawo ƙarshen waɗan nan hare-hare saboda ba mu san waye abin hari na gaba ba."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Wadannan hare-haren da tuni suka mamaye mafi yawan kananan hukumomin yankin (wato Shinkafi, wasu sassan Birnin Magaji, Zurmi da Kaura Namoda) suna ta karuwa a kaikaice."
"Hare-haren sun fi munana a ƙauyukan Dagwarwa, Walo, Disko, Dayau, Abaniyawa, Kabaje, Alko da sauransu saboda sun zama tamkar maɓoyar 'yan bindiga."
"Waɗan nan 'yan ta'adda suna fitowa su yi yawo kamar kowa cikin walwala musamman a garuruwan Abaniyawa, Kabaje, alko da kuma Dayau."
Tasirin da hare-haren ya yi
Kungiyar ta ce hare-haren ta'addancin da 'yan fashin suke kaddamar wa ya kawo koma baya a harkokin ilimi da tattalin arziki a cikin waɗan nan garuruwa, Daily Trust ta ruwaito.
Ta ƙara da cewa a kowane lokaci matafiya na cikin haɗarin yuwuwar yin garkuwa da su yayin da mahara ke yawan sace mutane da yawa da ke rayuwa a yankin.
A wasiƙar mai dauke da kwanan watan 19 ga watan Oktoba, 2023, sun ja hankalin shugaban ƙasa da gwamna Lawal cewa:
"Idan har ba a ɗauki mataki kan hare-haren ba, ba wai asarar rayuka da dukiyoyi ƙaɗai zai haifar ba, zai durƙusad da tattalin arziƙi da walwala a Zamfara ta arewa da ma jihar baki ɗaya."
Malam Kabiru, mazaunin Ƙauran Namoda ya tabbatar wa Legit Hausa cewa sun rubuta wannan wasiƙa kuma sun aika wa gwamnatin jiha da ta tarayya.
A cewarsa, lamarin tsaro a garuruwan da suke rayuwa ya kai maƙurar taɓarɓarewa amma suna sa ran wannan sako ya jawo hankalin masu riƙe da madafun iko.
"Ni a Ƙaura nake (Watau Ƙauran Namoda) Kuma wannan magana gaskiya ce. Amma Muna fatan za su yi abinda ya dace kuma za a dace da yardar Allah."
Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 9 a Katsina
A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun kai wani ƙazamin hari a garin Danmusa, hedikwatar ƙaramar hukumar Danmusa a jihar Katsina.
Miyagun ƴan bindigan dai sun kai farmakin ne a daren ranar Lahadi, 22 ga watan Oktoba inda suka halaka mutum tara.
Asali: Legit.ng