Reno Omokri Ya Fallasa Katobarar da Buhari Ya Yi Wa Kasar Nan

Reno Omokri Ya Fallasa Katobarar da Buhari Ya Yi Wa Kasar Nan

  • Tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya fallasa katoɓarar da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi a ƙasar nan
  • Reno Omokri ya bayyana cewa Buhari ya karɓe kuɗaɗen man fetur da ake siyarwa yanzu haka a ƙasar nan kuma ya kashe kuɗaɗen
  • A cewarsa da ƴan Najeriya za su iya arba da Buhari a bainar jama'a da sun huce fushinsu a kansa

FCT, Abuja - Tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, Reno Omokri a ranar Asabar, 21 ga watan Oktoban 2023, ya yi tsokaci kan katoɓarar da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wa ƙasar nan.

Reno Omokri ya bayyana cewa da ƴan Najeriya sun san abin da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi, za su iya huce fushinsu a kansa idan suka yi arba da shi a bainar jama'a.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Fadi Abu 1 da Zai Faru da Jihohin Kasar Nan da Ba a Cire Tallafin Man Fetur Ba

Reno Omokri ya fallasa Buhari
Reno Omokri ya fallasa katobarar da Buhari ya yi Hoto: Muhammadu Buhari, Reno Omokri
Asali: Twitter

Tsohon hadimin na tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, yayin da yake tsokaci a kan halin da darajar naira ta tsinci kanta a ƙasar nan.

Omokri ya ce wa masu cewa ya kamata Babban Bankin Najeriya (CBN) ya koma kare Naira da $1.5bn a duk wata, "Ina kuɗin za su fito?"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Buhari ta cinye kuɗin man fetur

Ya ce gwamnatin Buhari ta yi musanya da ɗanyen mai domin sayarwa a nan gaba, inda ya ce tuni sun karɓi kuɗin "Man da muke siyarwa yau har zuwa ƙarshen shekara sun karɓi kuɗin sun kashe."

Omokri ya ƙara da cewa:

"Babu wani kuɗin shiga da ke shigowa a halin yanzu, sai kudaden da ake aikowa daga ƙasashen waje. Idan ƴan Najeriya sun san abin da Buhari ya yi, za su iya huce fushinsu a kansa idan aka gan shi a bainar jama'a."

Kara karanta wannan

"Furuci Na Kishin Kasa": Shehu Sani Ya Yi Martani Bayan LP Ta Ce Yan Majalisunta Su Ki Karbar Motocin N160m

"Wataƙila shi ya sa ya ce zai yi ritaya zuwa Jamhuriyar Nijar. Amma juyin mulkin da aka yi a can ya ɓata shirinsa. Najeriya a yanzu ta lalace! Ba haka kawai gwamnatin Buhari ta buga tiriliyan nairori ba.
“Kuɗin da ba su da goyon baya fiye da takarda kawai. Babu zinari a CBN ko asusun rarar ajiyar waje da zai goyi bayan buga kuɗin da aka yi. Kuma ƴan Najeriya ba su sani ba, wasu jami'ansa da suka taimaka masa ya tafka wannan ta'asa sun fice daga ƙasar, ƴan jarida ku yi aikin ku. Wannan gwamnatin ba ta magana domin APC ba za ta iya fallasa APC ba!"

An Daure Magidanci Saboda Buhari

A wani labarin kuma, wani magidanci ya samu hukuncin ɗauri daga kotu bayan ya ƙulla auren bogi tsakanin surukarsa da tsohon Shugaba Muhammaɗu Buhari.

Kotun ta yankewa Gambo Adamu hukunci watanni 12 a gidan gyaran hali saboda damfarar surukar tasa da ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng