Yan Sandan Kasar Saliyo Sun Kama Wani Dan Najeriya Da Ake Nema Ruwa a Jallo Kan Laifin Kashe Budurwa
- Yan sandan kasar Saliyo sun kama wani dan kasuwar Najeriya da ake nema ruwa a jallo, Nnanyereugo Best, kan kashe budurwarsa
- Rundunar yan sandan jihar Lagas ta ayyana neman Nnanyereugo bayan ya kashe budurwarsa, Augusta Osedion
- Wanda ake zargin ya kashe kudi kimanin $25,000 don samun fasfot din kasar Saliyo, da samawa kansa sabuwar rayuwa tare da sauya bayanansa
Yan sanda sun kama wani dan kasuwa da aka ayyana nemansa ruwa a jallo, Nnanyereugo Best, a wani gidan rawa a garin Free Town, babban birnin kasar Saliyo.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Lagas, Benjamin Hundeyin, @BenHundeyin, ne ya ayyana neman Nnanyereugo kan kashe budurwarsa Augusta Osedion, dalibar jami'ar Lead City da ke Ibadan.
Wani mai amfani da dandalin X, @ENIBOY, wanda ya yada labarin, ya ce Nnanyereugo ya biya sama da $25,000 don siyan fasfot din Saliyo.
An kama shi ne bayan wani ya gane shi sannan ya tuntubi lauya mai kare hakkin dan adam, Femi Falana, wanda ya sanar da rundunar yan sandan jihar Lagas ci gaban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"An kama wani dan kasuwa Nnanyereugo Best, wanda @BenHundeyin ya ayyana nemansa kan kashe budurwarsa, Augusta Osedion, da libar jami'ar Lead City, a kasar Saliyo. Bayan ya aikata laifin, ya kashe fiye da $25,000 wajen siyan fasfot din Saliyo.
"Ya sauya sunansa zuwa Kanu Princeton Samuel. Dangin budurwarsa sun sanya hotonsa a soshiyal midiya. Wani a Saliyo ya gane shi. An untubi Mista Femi Falana sannan ya sanar da yan sandan Lagas da suka ayyana nemansa. An kama shi a wani gidan rawa a Free Town a jiya.
"Domin karin haske, $25,000 din ba wai na fasfo din Saliyo kadai ba ne illa abin da ya kashe kenan don samawa kansa sabuwar rayuwa da kuma canza sunan sa.”
Yan sanda sun kama shugaba da mataimakin shugaban makaranta kan dukan dalibi har lahira a Zaria
A wani labarin, an kama shugaba da mataimakin shugaban makarantar Al-Azhar da ke Zaria, jihar Kaduna kan zargin dukan dalibin JSS3, Marwanu Nuhu Sambo har lahira.
An yi zargin cewa wadanda ake zargin sun hadu sun yi wa Sambo hukunci mai tsanani wanda ya yi sanadiyar mutuwarsa a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba, rahoton The Nation.
Asali: Legit.ng