Yadda Aka Yi Jana'izar Ambasadan Najeriya Na Morocco a Jigar Kaduna

Yadda Aka Yi Jana'izar Ambasadan Najeriya Na Morocco a Jigar Kaduna

  • Daga ƙarshe, an yi wa marigayi Magajin garin Zazzau Sallar jana'iza kuma an kai shi makwancinsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada
  • Gwamnan Kaduna, Uba Sani, Malam Nasiru El-Rufai da shugaban majalisar wakilan tarayya sun halarci jana'izar a Zariya
  • Malam Uba Sani ya ayyana Alhaji Mansur Nuhu Bamalli da mutumin kirki kana ya yi masa addu'ar samun rahama

Zaria, jihar Kaduna - An yi Jana'izar jakadan Najeriya a ƙasar Morocco, marigayi Alhaji Mansur Nuhu Bamalli, a garin Zariya da ke jihar Kaduna.

Ɗaruruwan mutane ne suka yi tururuwa suka halarci Sallar Jana'izar marigayin daga ciki da wajen jihar Kaduna.

Jana'izar marigayi Sarkin Zazzau.
Yadda Aka Yi Jana'izar Ambasadan Najeriya Na Morocco a Jigar Kaduna Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Dubbanin mutanen ne suka yi cincirindo a fadar mai martaba Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli, domin jajanta wa iyalai da dangin marigayin.

Sun ayyana marigayin Mansur Bamalli, wanda shi ne Magajin garin Zazzau da mutumin kirki kuma mai cikakkiyar kamala.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Kwastam

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan mutanen da suna halarci jana'iza

Daga cikin manyan jiga-jigan da suka halarci wurin janazar har da mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani da tsohon gwamna, Malam Nasiru El-Rufai.

Shugaban majalisar wakilan tarayya, Tajudeen Abbas da Ministan muhalli na ƙasa, Balarabe Lawal Abbas na cikin ƙusoshin gwamnatin da suka halarci janaza.

Gwamnan Kaduna ya wallafa Hotunan wurin sallar jana'iza a shafinsa na Facebook da yammacin ranar Jumu'a.

Marigayi Ambasada Mansur Nuhu Bamalli wanda ƙani ne ga Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli ya rasu a wani asibiti na kudi da ke jihar Legas.

Ya rasu yana da shekaru 53 a duniya kuma ya bar mata ɗaya da kuma 'ya'ya guda biyu.

Har zuwa lokacin da Allah ya karɓi rayuwarsa, ya kasance Magajin Garin Zazzau, kuma babban jigo a Majalisar Masarautar Zazzau da ke jihar Kaduna a Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Mansur Bamalli: Muhimman Abubuwa 4 da Ya Kamata Su Sani Game da Marigayi Magajin Garin Zazzau

Da yake jawabi bayan sallar jana’izar, Gwamna Uba Sani ya bayyana marigayi jakadan a matsayin cikakken mutum na gari, ya kuma yi addu’ar Allah masa rahama.

Musulunci Ya Samu Karuwa

A wani rahoton na daban kuma Wata matashiyar budurwa mai suna Blessing ta bar addininta na kiristanci inda ta karbi addinin Musulunci hannu bibbiyu.

Addinin Musulunci ya samu karuwar wata matashiyar budurwa yar shekaru 18, mai suna Blessing, kuma ta sauya sunanta inda ta koma 'Khadijah' a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262