Kwamitin Masallacin Abuja Ya Karyata Jita-jitar Cewa Za a Rushe Bangaren Masallacin
- Kwamitin gudanarwa na babban masallacin Abuja ya fitar da sanarwa kan jita-jitar rushe bangaren masallacin a Abuja
- An yi ta yada labarin cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya shirya rushe bangaren masallacin don fadada hanya da ta biyo kusa da masallacin
- A cikin sanarwar, kwamitin ya musanta wannan labari da ake yadawa inda ya bukaci al'ummar Musulmai su yi watsi da shi
FCT, Abuja - Kwamitin babban masallacin Abuja ya bukaci al'ummar Musulmi da su guji bata sunan ministan Abuja, Nyesom Wike.
Limamin masallacin, Dakta Muhammad Kabir Adam da daraktan kudi, Ambasada Haliu Shu'aib su suka bayyana haka yayin ganawa da manema labarai.
Meye kwamitin masallacin Abuja ya ce kan jita-jitar?
A ganawar wanda Sakataren hukumar FCDA, Injiniya Shehu Hadi ya shirya, sun karyata cewa za a rusa bangaren masallacin, Legit ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar wanda Wike ke jagoranta tun farko ta musanta zargin wanda daga bisani kwamitin masallacin ya tabbatar.
Sanarwar ta ce:
"Hukumar masallacin Abuja ta samu labarin da ya ke yawo na shirin rushe bangaren masallacin wanda ke jawo hatsaniya a tsakanin al'ummar Musulmai.
"Ya kamata mutane su yi watsi da wannan labarin kanzon kurege da ake yadawa."
Meye ya jawo kace-nace kan masallacin Abuja?
Wannan na zuwa ne bayan jita-jitar da ake yadawa na shirin rushe bangaren masallacin don fadada hanya, cewar Vanguard.
Al'ummar Musulmai sun yi tir da Allah wadai da wannan kudiri inda su ka zargi ministan Abuja, Wike da nuna tsantsar kiyayya ga addinin Musulunci.
A martaninshi, Wike ya ce ko kadan ba ya gaba da Musulunci inda ya ce babu wanda ya ke martabawa fiye da kowa kamar Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar.
Wike: Fasto ya roki Tinubu ya kama Gumi
Kun ji cewa, Fasto Elijah Ayodele ya bukaci Shugaba Tinubu ya kama Sheikh Ahmed Gumi saboda kalamansa kan ministan Abuja, Nyesom Wike.
Faston ya ce Gumi na son tayar da hankali da kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan kasar.
Sheikh Gumi ya ambaci Wike da shaidanin mutum inda ya bukaci Shugaba Tinubu ya sauya shi da Musulmi don dakile shirinsa na rushe Musulunci.
Asali: Legit.ng