Jakadan Najeriya a Morocco, Alhaji Mansur Nuhu Bamalli, Ya Rasu
- Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya yi wa jakadan Najeriya a Morocco, Alhaji Mansur Nuhu Bamalli, rasuwa
- Marigayin shi ne Magajin Garin Zazzau kuma ƙanin mai martaba Sarkin Zazzau, ya rasu ne a asibitin Kudi a jihar Legas
- Masarautar Zazzau ta fitar sanarwan cewa nan gaba kaɗan za a sanar da lokacin jana'izar marigayin
Zaria, Jihar Kaduna -Alhaji Mansur Nuhu Bamalli, Jakadan Najeriya a ƙasar Morocco ya riga mu gidan gaskiya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Marigayin shi ne Magajin garin Zazzau a jihar Kaduna kuma ɗan uwa na jini, ƙanin Mai Martaba Sarkin Zazzau.
Wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na Masarautar Zazzau ya fitar, ta ce Mansur Nuhu Bamalli, ya rasu ne a wani Asibitin kuɗi a jihar Legas a hanyarsa ta zuwa Morocco.
Gwamnan Arewa Ya Waiwayi Leburori, Ya Ce Zai Ɗauki Nauyin Karatunsu Har Su Gama Jami'a Bisa Sharaɗi 1
Sanarwan ta ƙara da cewa, "Za a sanar da lokacin da za a masa sutura nan ba da jimawa ba."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya rasu ya bar mata ɗaya da 'ya'ya biyu. Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa shi Jakadan Najeriya a Morocco sheƙara ɗaya da ta wuce.
Yadda aka naɗa shi jakadan Najeriya
A wata takarda mai dauke da kwanan watan 7 ga watan Oktoba, 2022 da sa hannun ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ya ce nadin nasa ya zo ne bisa la’akari da shekarun da ya ɗauka yana hidima.
“Za a gayyace ka nan gaba kaɗan don bikin rantsarwa. Muna fatan ka karɓi gaisuwar fatan alheri na Minista da Babban Sakatare da dukkan ma’aikatan Ma’aikatar,” in ji takardar.
Kafin wannan nadin da aka masa ya kasance mataimakin darakta a ma'aikatar harkokin waje, kamar yadda PM News ta ruwaito.
Ma'aikatar ƙasashen waje ta sauke tare da kiran kowane jakada a faɗin duniya amma shi har yanzun bai dawo Najeriya ba saboda bai warware harkokin kuɗin tafiya ba.
Tsohon DG Na Ofishin Kasafin Kuɗin Najeriya, Bode Agusto, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
A wani rahoton na daban Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Bode Agusto, tsohon DG na ofishin kasafin kuɗin tarayya ta rasu yana da shekaru 68 a duniya.
Mista Olufemi Awoyemi, Shugaba kuma mamallakin kamfanin Proshare Nigeria ne ya sanar da rasuwar ranar Alhamis, 19 ga watan Oktoba, 2023.
Asali: Legit.ng