Shugaba Tinubu Ya Soke Naɗin Matashin Shugaban Hukumar FERMA
- Bola Ahmed Tinubu ya yi amai ya lashe kan naɗin Injiniya Imam Kashim Imam a matsayin shugaban hukumar FERMA na ƙasa
- A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Tinubu ya soke naɗin da ya yi wa matashin ɗan kimanin shekaru 24 a duniya
- Sanarwan ta yi bayanin cewa wannan matakin bai shafi sauran mambobin majalisar gudanarwar FERMA da aka naɗa ba
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin a janye naɗin da ya yi wa Injiniya Imam Kashim Imam, a matsayin shugaban hukumar gyaran tituna (FERMA).
Dama naɗin da shugaban ƙasa ya yi wa matashin ɗan shekara 24 a duniya wanda bai jima da kammala digiri ba ya haddasa cece kuce mai zafi a faɗin ƙasar nan.
Sai dai mai magana da yawun shugaban ƙasa, Chief Ajuri Ngelale, a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja, ya sanar da cewa Tinubu ya soke naɗin Imam.
A sanarwan da aka wallafa a shafin Tuwita watau X, Ngelale ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Shugaban ƙasa ya janye wannan naɗin da aka ambata a sama kuma matakin zai fara aiki nan take."
"Wannan mataki bai shafi sauran naɗe-naɗen mambobin majalisar gudanarwa ta FERMA ba."
Abin da ya biyo bayan naɗin Imam a matsayin shugaban FERMA
Bayan sanar da naɗa Kashim Imam a matsayin shugaban hukumar FERMA, wasu yan Najeriya sun yaba wa shugaban ƙasa yayin da wasu kuma suka caccake shi.
A cewar wadanda suka yi watsi da nadin matashin, Imam bai da jajircewa da gogewar da zai iya jagorantar wata babbar hukuma mai girma kamar FERMA.
Ƙalilan daga cikin 'yan Najeriyan da suka goyi bayan naɗin sun bayyana cewa wannan wata dama ce ga saurayin ta yadda zai koyi aiki kuma ya samu gogewa.
"Furuci Na Kishin Kasa": Shehu Sani Ya Yi Martani Bayan LP Ta Ce Yan Majalisunta Su Ki Karbar Motocin N160m
Tinubu Ya Sallami Shugabannin NBC, NAN Da NTA, Ya Nada Sabbi
A wani rahoton na daban Shugaba Bola Tinubu ya yi sabbin nade-nade a Ma’aikatar Yada Labarai da Hukumar Wayar da Kan Jama’a.
Tinubu ya yi sabbin nade-naden ne har guda takwas wadanda za su yi aiki karkashin ma’aikatar Yada Labarai.
Asali: Legit.ng